Shin yarjejeniyar zaman lafiyar Zamfara ta wargaje ne?

Jihar Zamfara

Asalin hoton, TWITTER/NIGERIAN ARMY

An wallafa

Bayan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, mutane da dama na nuna fargabar cewa yarjejeniyar sulhu da gwamnatin jihar ta kulla da 'yan bindgar domin su ajiye makamansu na neman wargajewa.

A jiya ne dai aka kai hari garin kuma suka kashe mutane akalla goma sha takwas.

Hukumomi dai sun bayyana cewa ga alama harin na ramuwar gayya ne bayan da 'yan sintiri da ake kira 'yan sa-kai suka kashe 'yan bindiga kimanin goma a farkon wannan wata.

Mai bai wa gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan lamuran tsaro, Abubakar Muhammad Dauran, ya shaida wa BBC cewa yarjejeniyar ba ta wargaje ba tana nan tana aiki.

Bayanan sautiShin yarjejeniyar zaman lafiyar Zamfara na aiki?

Ya kuma ce gwamnati a shirye take ta ci gaba da karbar makaman, haka kuma ta bai wa shugabannin fulani umarnin karbe makamai daga hannun matasansu.

Jihar Zamfara dai ta yi fama da matsalolin tsaro sosai a shekarun da suka gabata, amma sun fara daidaita tun bayan hawan gwamna Bello Matawalle kan karagar mulki.

Barayin daji sun hau teburin sasantawa da gwamnati wanda ake ganin ya yi tasirin tabbatuwar zaman lafiya a jihar.