Hotuna: Rayuwar masu kwasar shara da masai na Indiya

An wallafa

Sudharak Olwe ya bi rayuwar masu kwasar shara a Mumbai tsawon shekaru 20n.

Su kan yi ayyukansu a yanayi mai muni, kuma mafi yawan wadanda suke irin wannan aikin 'yan wata kabila ce da ake kyama kuma wadanda aka tsangwama.

Kuma rayuwarsu ta kasance a haka, duk da ci gaban da Indiya ta samu a fannin tattalin arziki da zamantakewa da fasaha.

An nuna hotunan Olwe na baya-bayan nan a wani bangare na bikin Ranar Makewayi ta Duniya ta shekarar 2019, da kungiyar tabbatar da tsaftar muhalli ta WaterAid ta shirya.

A close up of the legs of sanitation workers with a broom
Sanitation Workers in Panna, India

Masu kwashe datti daga al'ummar Valmiki na cire bahaya da hannunsu daga masai a Amanganj, Panna, Madhya Pradesh.

Amanganj Sanitation Workers in Panna at night

Betibai Valmiki ta ce: "Ba a yadda mu sha shayi a ko wane gidan cin abinci a nan.

"Ko mun je kananan shagunan shan shayi, sai dai a zuba mana a kofunan roba wanda da mun sha ake zubar da su yayin da sauran mutane ake zuba masu a kofunan shan shayi na tangaran."

Mafi yawan matan na fama da cutar asma da maleriya- amma babu kiwon lafiya kuma ana hana su albashinsu idan ba su da lafiya.

42-year-old Mukeshdevi, a woman manual scavenger, with her husband Sukhraj , mother in-law, five children and two grandchildren in Meerut's Bhagwatpura, India

Mukeshdevi mai shekaru 42 tare da mijinta Sukhraj da uwar mijinta da 'ya'yanta biyar da jikokinta biyu a Bhagwat Pura, Meerut, Uttar Pradesh na samun rupee 2,000 (Dala 20) a ko wane wata.

Mukeshdevi veils her face and hair with her dupatta

"Ya ya za mu yi?" a cewarta.

"Ko da za mu bude shagon sayar da shayi, babu wanda zai siya a wajenmu saboda mu Valmikis ne."

Sanitation workers in Amanganj in Panna district, India

Santosh na aiki a Amangank tare da matarsa da 'ya'yansu biyu.

A shekarar 1992, ya kusa nutsewa a lokacin da ya ke yasar wata masai tare da abokan aikinsa, kuma daya daga cikinsu ya mutu.

Ashe masan na da zurfin gaske, amma sai aka ce masu ba shi da zurfi.

Sai dai duk da idanuwansa sun lalace gaba daya, ba a taba biyansa diyya ba.

A bayan rigar da ya sa, an rubuta kalmar "Dan Adam".

Sanitation workers, Geeta Mattu, Sashi Balmeek and Raju Dumar, in Panna District, India.

A Agra Mohalla, Panna Geeta Mattu, Sashi Balmeek da Raju Dumar suna aiki kullum daga karfe biyar na safe zuwa karfe daya na rana kan rupee 7,000 a wata.

In Agra Mohalla in Panna District, Geeta Mattu finds a dying injured cow near an open garbage point.

"Babu mutunci a cikin wannan aikin." in ji Geeta.

"Ana wulakanta mu. Ba a taba yi mana godiya."

People of the Dom community

A watan Afrilun bara, al'ummar Dom a wajen garin Tillai gaon, Bihar, sun yi asarar gidaje 10 da mafi yawan shanunsu a wata gobara.

Suna aiki a garin Sasaram da ke makwabtaka amma saboda sun rasa takardunsu na shaida basu samu kudin diyyarsu ba.

Meenadevi, from the Dom community, cleans dry latrines in a Muslim neighbourhood

Meenadevi mai shekaru 58 na daukar bahaya daga wata unguwar musulmi a Rohtas.

Ta fara aiki ne a matsayin mai kwasar bahaya shekaru 25 da suka wuce tare da uwar mijinta.

"Daga farko, na kan ji matukar kyama," ta ce.

"Ban shirya ba kuma na ji kunyar yin aikin saboda tsangwamar da ke tattare da shi.

"Amma yanzu na saba da warin.

"Talauci ba ya barin mutum ya zabi yadda zai yi.

Meenadevi, from the Dom community, cleans dry latrines in a Muslim neighbourhood in Bihar's Rohtas district.

"Uwar mijina ta mutu tana aikin nan.

"Ta kan dauki bahayar a gwangwanaye. Ni ma kuma hakan nake yi da.

"Yanzu ba ma amfani da gwangwanaye. Amma duk da haka, ni ma abin da zai same ni kenan".

Duka hotunan hakkin mallakar Sudharak Olwe da WaterAid ne