Faransa ta mayar wa Senegal kayan tarihin wani Malamin Islama

An wallafa

Faransa ta mayar wa da Senegal wasu kayan tarihi wadanda mallakar wani sanannen malamin addinin Islama ne da ya yi zamani a karni na 19.

Wannan dai wani yunkuri ne da Faransar ke yi na ganin ta mayar wa Senegal duk wani kayan tarihi da ta mallaka da kuma aka karbe a lokacin mulkin mallaka.

Firai Minista Edouard Philippe ne ya mika wa Shugaba Macky Sall wani gariyo da kuma takobin katako da ke cikin kube.

An gano cewa ainihin kayan yakin na tarihi mallakar Shugaba Umar Saidou Tall ne, wanda ya yaki mulkin mallaka da Faransa ta yi wa Senegal.

Mista Phillipe ya ce wannan sharar fage ne kan abin da ya kira shirin mayar wa Senegal da kayanta da yanzu haka ke ajiye a gidan tarihin Faransa.

"Wannan rana ce ta tarihi," in ji shugaban Senegal. Wasu daga cikin zuri'ar Omar Saidou Tall sun halarci bikin bayar da kayayyakin.

Mista Philippe ya ce shi ne "matakin farko" na aikin mayar da kayayyakin tarihi na Senegal da ke gidan adana kayan tarihi na Faransa, inda ake ajiye da kayayyaki a kalla 90,000 na kasashen kudu da Hamadar Sahara.

A shekarar da ta gabata ne wata tawagar kwararru bisa umarnin Shugaba Emmanuel Macron, suka bayar da shawarar ya kamata a mayar da kayan tarihin Afirka da ake ajiye da su a gidan adana kayan tarihin Faransa.

Rahoton da suka gabatar wa gwamnati ya nuna cewa yawancin kayan tarihin Afirka kusan 46,000 suna gidan adana tarihi na Quai Branly da ke Faransa.

''Daman kayanmu ne da aka dauka, yanzu kuma an dawo mana da abinmu,'' inji shugaban gidan adana kayan tarihi na Black Civilisations a birnin Dakar, Hamady Bocoum, kamat yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP

An adana takobin da aka yi da karfe na cikin kwanson fata a gidan adana kayan tarihi na Faransa, amma bikin na ranar Lahadi ya nuna an dawo da abin cikin shekara biyar.

Mataki na gaba shi ne 'yan majalisar Faransa su kada kuri'ar kan ko dai a mayar da kayan baki daya ko akasin haka.

Shin wanene Omar Saidou Tall?

Shi dai El Hadj Omar Saidou Tall dan siyasa ne, kuma kwamandan soji kuma fitaccen malami da ya jagoranci kungiyar 'yan uwa musulmi ta Tidjane, mabiya mazahanar Sufaye a yammacin Afirka.

Ya yi yaki da sojin Faransa daga shekarar 1857 zuwa 1859, kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a shekarar 1860.

Kamar yadda masana tarihi na Senagal suka tabbatar, malamin ya yi batan dabo daga garin Bandiagara na kasar Mali.

A shekarar 1836 zuwa 1897 dansa Ahmadou, ya gaje shi amma a watan Afirilun shekarar 1893 Faransa ta hambarar da shi a garin Bandiagara.

A nan ne sojin Faransa suka karbe takobinsa, wanda aka yi ta mai kaifin gaske, saman kanta kuma yana da tsini kamar bakin tsuntsu.

Turawan mulkin mallaka na Faransa sun kuma sace littafan malamin, kamar yadda daya daga cikin dalibansa El Hajj Mamadou Mactar Thiam ya bayyana.

''Sun sace komai nasa, ciki har da kayan dakin karatunsa da ke Segou, yanzu da Faransa ta fara kokarin dawo da takobinsa ina fatan sauran kayan su ma za su dawo gida,'' in ji Thiam.