Rikici ya lafa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa

Asalin hoton, Reuters
Da alama Isra'ila da kungiyar Islamic Jihad na mutunta shirin tsagaita wuta da suka kulla duk da wasu hare-haren roka da ke aukuwa jefi-jefi.
Yarjejeniyar ta kawo karshen fadan da aka gwabza na kwana biyu, fadan da yayi sanadin mutuwar Falasdinawa 34, cikinsu har da mata uku da kananan yara takwas, kuma ya hana kowa motsawa a wasu sassan Isra'ila.
Dakarun Isra'ila sun ce 25 cikin wadanda ta kashen 'yan tawaye ne.
Wannan sabon rikicin ya barke ne ranar Talata bayan da aka kashe Baha Abu al-Ata tare da matarsa a wani hari da Isra'ila ta kai da jiragen yaki.
Ana daf da sanar da tsagaita wuta ne wani hari da sojojin sama na Isra'ila suka kai ya kashe mutum takwas, wadanda dukkansu 'yan gida daya ne a birnin Gaza.
Kusan kullum ka ji ana jana'iza a Gaza. Sai dai a janazar da ake yi, akwai kananan yara biyar na cikin wadanda ake birnewa.
Isra'ila ta ce mai gidan da ta kai hari kansa kwamanda ne a kungiyar Islamic Jihad.
Amma wani makwabcinsa da ya je kallon manyan ramukan da rokokin da suka fada wa gidan suka yi, na da wani bayani na daban:
"Da tsakar dare wajen karfe 12:30 ne wasu jiragen yakin Isra'ila su ka kai wa wannan wurin hari, kan wadannan kananan gidajen gonar da ke nan," inji mutumin.
Ya kuma kara da cewa "Kuma a sanadiyyar haka suka kashe fararen hular da basu ji ba, ba su gani ba. Na san mamatan sosai, kuma babu abin da ya hada su da batun turjiya."

Asalin hoton, Reuters
Wannan harin ya kasance irinsa mafi muni cikin kwanaki biyun da aka dauka ana gwabza fada, rikicin da ya samo asali bayan da aka kashe wani kwamandan kungiyar Islamic Jihad.
Daya daga cikin bukatun kungiyar kafin ta daina kai hare-hare shi ne Isra'ila ta daina kai hare-hare da niyyar hallaka jagororin masu nuna adawa da gwamantin ta Isra'ila.
Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ya ce babu inda aka yi wa Falasdinawa alkawarin daina kai hare-haren, amma da alama dukkan bangarorin na mutunta tsagaita wutar da ke ci a yanzu.
Wannan fadan bai sauya komai ba a yankin na Gaza, face cewa kungiyar Hamas mai iko da yankin ba ta shiga cikin rikicin ba.

Asalin hoton, AFP












