Zanga-zangar neman a saki Sowore a Landan

Bayanan bidiyo, Yadda aka yi zanga-zangar neman sakin Sowore a Landan
An wallafa

Wasu masu zanga-zanga a gaban Abuja House a Landan sun nemi gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin dan gwagwarmayar a Najeriya Omoyele Sowore.

Fiye da wata uku ke nan hukumar DSS ta kasa ta tsare shi bayan da ya shirya wata zanga-zangar da aka yi wa lakabi da #RevolutionNow, inda hukumomi ke tuhumar sa da laifukan da suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'ammali da kudi ta hanyar ba bisa ka'ida ba.