Kasashen duniya na nazari kan tsadar kujerar hajji

Bayanan sautiKasashen duniya na nazari kan tsadar kujerar hajji
An wallafa

Latsa lasifikar da ke sama don sauraron bayani daga bakin wakilin Najeriya a wajen taron, Malam Bashir Muhammad:

Wakilan kasashen duniya sun hadu a Burtaniya domin yin bita kan matsaloli da kalubalen da ake cin karo da su yayin aikin Hajji da Umrah.

Wakilan kasashen suna tattaunawa tare da bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a inganta da kuma magance matsalolin.

Kuma daga cikin muhimman batutuwan da ake tattaunawa har da tsadar kudin hajji.

Malam Bashir Muhammad na daga cikin mahalarta taron a matsayin wakili daga Najeriya, ya kuma yi wa Nabila Mukhtar Uba karin bayani kan yadda taron na yini uku ke gudana.