Granit Xhaka: Kyaftin din Arsenal ya ce 'Na kai makurar fushi'

An wallafa

Kyaftin din Arsenal, Graint Xhaka ya ce an kai shi kwano sakamakon barazanar da ake ci gaba da yi wa matarsa da 'yarsa, kamar yadda fushinsa ya bayyana karara kan magoya bayan kungiyar a ranar Lahadi.

An ta yi wa dan wasan kasar Switzerland din ihu lokacin da aka sauya shi kuma ya ke fita daga filin wasa, abin da ya sanya shi toshe kunnensa a matsayin martani.

A wani bayani da ya yi mai taba zuciya, dan wasan ya ce "abin ya matukar taba zuciyata" saboda irin sakonnin da aka yi ta aikewa ta kafofin sada zumunta kan wasannin baya-bayan nan.

Suna rubuta 'ka kashe matarka' da kuma 'muna fatan 'yarka ta kamu da ciwon kansa'.

A karan farko da ya yi magana kan al'amarin, Xhaka mai shekaru 27, ya ce "fushi ne ya dauke shi" har ya mayar da martanin "rashin girmamawa" ga magoya bayan.

Kocin kungiyar, Unai Emery ya nemi dan wasan ya fito fili ya nemi ahuwa kan abin da ya aikata.

Sai dai dan wasan ya cije yana cewa yana mai bada hakuri idon mutane na zaton abin da ya yi ba dai-dai ba ne.

"Abin da ya faru yayin sauya ni ya matukar harzuka ni" a wani bayani da ya wallafa a Instagram, ranar Alhamis, Xhaka ya ce "ina son wannan kungiya kuma ina ba da cikakkiyar gudunmawa a ciki ko a wajen fili ga kungiyar.

"Magoya baya ne ba su fahimci yadda nake ji ba, game da zagin da suka yi ta yi yayin wasa da kuma a kafafen sada zumunta kan wasan makon jiya da kuma watannin baya, abin ya matukar harzuka ni.

"Mutanen na ta cewa " 'sai mun karya kafafunka, 'gwara ka kashe matarka' 'muna fatan 'yarka ta kamu da ciwon kansa' hakan ya matukar ruda ni, ya kaini matukar kurewa har sai da naji ina son ramawa.

"Fatana shi ne alakarmu ta koma yadda take ta girmamawa, mu tuna me ya sa mu son wannan wasannin tun farko, mu yi yadda za mu samu ci gaba tare."

Ba dai wannan ne karon farko da magoya suka yi wa Xhaka ihu ba a wannan kakar wasannin, shi kuma Emery na fitowa fili yana kare dan wasan, har bayan wasan da suka yi da Aston Villa a watan jiya.

Har yanzu dai Emery ya ki bayyana ko Xhakan zai ci gaba da rike kambun Kyaftin na kungiyar.