Najeriya ta kama hanyar zama mai jam'iyya daya tilo - APC

APC

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ikirarin cewa kasar ta kama hanyar zama mai jam'iyya daya tilo.

APC ta ce a matsayinta na jam'iyyar da ta yi imani da tsarin dimokradiyya da kuma siyasar kawo sauyi, ba za ta iya ci gaba da yaudarar kai da cewa komai na tafiya kalau ba.

Wata sanarwa da sakataren yada labaran APC, Mallam Lanre Issa-Onilu ya fitar ta ambato APC na cewa tsarin dimokradiyya ba zai tafi yadda ya kamata ba, idan jam'iyyar da ake dauka a matsayin babbar mai adawa wato PDP ta zama maras sanin ciwon kai da rashin alkibla.

Ta ce yayin da gwamnati mai ci ke tunkarar hanyoyin magance kalubalan kasar, da kuma a lokacin da ya kamata kowa ya mayar da hankali wajen gina kasa, abin da PDP da 'yan kan zaginta suka fi kauri bai wuce karkatar da hankula ba.

Dangane da wannan ikirari na jam'iyyar APC, Buhari Muhammad Fagge ya tuntubi masanin kimiyyar siyasa, Dr. Abubakar Kyari, don jin ko da gaske ne kasar ta kama hanyar zama mai jam'iyya daya tilo?

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar tasu:

Bayanan sautiHirar Dr Kari kan jam'iyya daya tilo