Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Malamin da BBC ta fallasa ya yi kurarin zuwa kotu
Wani malamin jami'a a kasar Ghana ya yi da baranzarar maka BBC a kotu.
Wani rahoton binciken kwakwaf da BBC ta yi ya bankado Farfesa Ransford Jampo yana neman yin lalata da wata daliba kafin yayi mata alfarmar samun gurbin shiga jami'ar.
Farfesa Ransford Jampo wanda ya yi kurarin daukar matakan shari'a a kan BBC, ya musanta zargin aikata laifi da hoton bidiyonsa da BBC ta nada cikin sirri kuma ta nuna a rahoton.
Sashen Binciken Kwakwaf na BBC Africa Eyen ne ya gudanar da bincike na tsawon shekara kan yadda wasu malaman jami'a ke amfani da matsayinsu wurin yin lalata da dalibai mata domin samun gurbin karatu ko cin jarabawa.
Rahoton wani bangare ne na binciken da wakiliyar BBC mai binciken kwakwaf Kiki Mordi ta yi shigar burtu a matsayin daliba mai neman gurbin karatu a jami'ar da Farfesa Ransford Jampo ke koyarwas.
Bayan fitar rahoton da BBC ta hada ne hoton bidiyon Farfesa Ransford Jampo da yadda dalibansa suka yi masa ihu a ajiya Litinin ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.
A bidiyon an ga malamin yana zubar da hawaye sannan ya fice daga ajin bayan ihun da daliban suka yi masa.
Daga baya Farfesa Jampo ya fitar da wani bidiyo inda a ciki yake bayyana cewa daliban nasa na jinjina masa ne bisa kokarinsa, abin da ya shi zubar da hawaye a gabansu.
Wakilin BBC ya ce jami'ar Ghana ba ta fitar da sanarwa game da lamarin ba tukuna.
Rahoton wanda ya yi tashe a shafukan zumunta a fadin duniya ya kuma haifar da tattaunawa inda jama'a suke ta bayyana ra'ayoyi mabambata.