Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata 'yan ci rani sun nutse a teku a Italiya
Akalla mata 13 ne ciki har da masu juna biyu suka nutse a hadarin kwale-kwalen da ya kife da 'yan cirani a Tekun Mediterranean.
Hukumomin Italiya sun ce matan sun mutu ne kafin isowar ma'aikatan ceto yayin da ake neman wasu mutum fiye da 12.
Jami'an sun ce jirign ya kife ne sakamakon rashin kyan yanayi a kusa da tsibirin Lampedusa da ke kasar Italiya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da 1,000 sun mutu a Tekun Mediterranean a wannan shekarar a kokarinsu na tsallakawa zuwa nahiyar Turai.
Masu tsaron teku a Italiya sun kaddamar da aikin ceto a ranar Lahadi bayan an sanar da su game da wani jirgi dauke da mutane fiye da kima a kusa da Lampedusa.
Bayan isar masu aikin ceto, mummunan yanayi ya sa jirgin 'yan ciranin kifewa, a cewar hukuma.
Kafar yada labaran kasar Italiya ta ce jirgin ya baro gabar Tunisiya ne dauke da mutum 50.
Masu aikin ceto sun yi nasarar tseratar da mutum 22 da tsamo gawarwakin mata 13. Daga cikin wadanda ba a gani ba akwai akalla kananan yara takwas, a cewar wadanda suka tsira.
Kamfanin dillancin labarai na Asna ya ruwaito cewa wani jami'in gwamnatin kasar Italiya ya isa wurin da hatsarin ya auku domin fara bincike.
Dubban 'yan gudun hijira na kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai a duk shekara. Yawancin wadanda ke isa Turan na yin tafiyar ne a cikin jirage masu matsala da daukar kaya fiye da kima.
Mutane da dama sun mutu a kan hanya.
A watan jiya, Faransa da Italiya sun bukaci a fitar da tsarin rarraba 'yan gudun hijira kai tsaye a kasashen nahiyar Turai, sakamakon karuwar 'yan gudun hijira da ke shiga Turai ta Italiya da Girka.