Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tashi daga taron Kamaru ba tare da cimma matsaya ba
Tattaunawar da aka kwashe mako guda ana yi a Kamaru kan yadda za a shawo kan batun ballewa daga jamhuriyar ya kare dutse a hannun riga.
Bangarorin biyu dai sun yi zargin cewa tattaunawar ta gaza cimma mafita ne saboda rashin masu shiga tsakani wadanda ba sa goyon bayan kowane bangare, da kuma kin amincewa da 'yancin cin gashin kai na yankin renon Ingilishi.
Shugaba Paul Biya ya ce za su martaba dukkanin shawarwarin da aka bayar a yayin zaman tattaunawar da suka hada da kiraye-kirayen kyale jama'ar yankin renon Ingilishi zabar shugabannin yankunansu.
A ranar Alhamis ne dai shugaba Paul biya ya yi umarnin sakin fursunoni fiye da 300.
To sai dai hakan bai gamsar da masu son ballewa daga kasar ba da masu ra'ayin sassauncin da ke cewa an daure dubban mutanen bisa tuhume-tuhumen karya.