Jacques Chirac: Hotunan jana'izar tsohon shugaban Faransa

Asalin hoton, AFP
Tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da Vladimir Putin na Rasha suna cikin tsofaffi da kuma shugabannin duniya masu-ci da suka halarci jana'izar Jacques Chirac, tsohon shugaban Faransa.
Wani rukunin mawaka ne ya yi ta rera waka yayin da tsohon dogarin tsohon shugaban ya ciccibi makararsa, wadda aka lullube da tutar kasar, zuwa cikin cocin Saint-Sulpice da ke birnin Paris.
Chirac ya rasu ne a makon da ya gabata yana da shekara 86.
Ya yi wa'adin mulki sau biyu a matsayin shugaban kasa. An ayyana Litinin a matsayin ranar makoki a kasar Faransa.
Daga cikin masu makokin, akwai dukkanin tsofaffin shugabannin Faransa uku wadanda ke raye - Giscard d'Estaing da Nicolas Sarkozy da Francois Hollande.
Sai kuma shugaba mai-ci Emmanuel Macron, wanda ya bayyana Chirac a matsayin "mutumin kirki" a makon da ya gabata.
A lokacin mulkinsa na farko ne (1995-2002), Jacques Chirac ya sanya Faransa cikin kasashe masu amfani da kudin bai-daya na euro.
A farkon mulkinsa na biyu kuma (2002-2007), ya jagoranci kasashen duniya wajen kin jinin yakin da Amurka ta kaddamar a kasar Iraki.

Asalin hoton, Corbis
Daga karshe-karshen rayuwarsa ya sha fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa, abin da ya sha musantawa.

Asalin hoton, AFP

Dubban mutane ne suka yi dogon layi domin kallon gawar tasa a karshen mako.

Asalin hoton, EPA
Wani lokacin layin yakan kai tsawon kilomita 1 duk da ruwan sama da aka rika yi.

Asalin hoton, AFP

Jama'a da dama sun rike lema saboda ruwan sama.

Asalin hoton, EPA
Bayan an fara ajiye shi a Les Invalides, an mika gawar tsohon shugaba Jacques Chirac zuwa cocin Saint-Sulpice domin bikin karshe na binne shi.

Asalin hoton, EPA













