Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikici tsakanin 'yan Najeriya da Kenya a kan Lupita
Fada ya kaure tsakanin 'yan Najeriya da takakwarorinsu na kasar Kenya a shafin Twitter saboda zabar wata jaruma 'yar kasar Kenya, Lupita Nyong'o ta fito a matsayin 'yar Najeriya a wani shirin fim.
Fim din mai suna Americanah, labari ne na wata mata 'yar Najeriya da ta je karatun jami'a a Amurka da kuma dawowarta Legas.
An samo labarin dake fim din Americanah ne daga wani littafi wallafar Chimamanda Ngozie Adichie, wanda ya yi fice har ya samu babbar kyauta a 2013.
Tun bayan sanarwar da kamfanin shirya fina-finai na WarnerMedia ta fitar a makon jiya, 'yan Najeriya ke ta nuna adawarsu a shafin twitter, cewa bai dace a zabi Nyong'o 'yar kasar Kenya, wacce ta taba lashe kyautar jarumar fim na Oscar ba, ta fito a matsayin 'yar Najeriya a fim din.
A cewarsu, zai fi dacewa a sanya 'yar Najeriya da za ta iya magana da harshen 'yan Najeriya ta fito a matsayin 'yar kasar.
"Fitowar Lupita a matsayin zai fuskanci matsala daya... magana da harshen Ibo," a cewar wani a twitter.
Wannan kuma na cewa: "Akwai kyawawan jarumai mata 'yan Najeriya da za su fi iya yin abun da ake bukata."
A nasu bangaren, 'yan Kenya a shafin twitter sun yi ta kare zabin da aka yi wa Nyong'o, inda suke wa 'yan Najeriya shagube da cewa ai ba Nyong'o ce ta "kawo rashin aikin yi a Najeriya ba" saboda ta zama kwararriyar jaruma.
Wasu kuma sun tunatar da 'yan Najeriyar cewa ba a sanya dan yankin gabashin Afirka ko daya ba a wakar Beyoncé da aka sanya fim din 'The Lion King' wanda kamfanin Disney ya sabunta, duk da cewa an yi amfani da yanayin kurmin kasar Kenya wajen tsara fim din.