Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Barayin fetur na sa kamfanin Shell asarar $560,000 kullum a Najeriya'
Kamfanin mai na Shell a Najeriya ya ce yana tafka asarar gangar mai 10,000 kowace rana a kasar sakamakon ayyukan masu fasa bututun mai da a kiyasce kudin da kamfanin ke asararsu ya kai dala dubu 560 kwatankwacin fam dubu 452 duk rana.
Asarar da masu fasa bututun man a yankin Neja Delta ke janyowa kamfanin na Shell a shekara ya kai dala miliyan 204.4.
Wannan sanarwar ta fito ne ta bakin Igo Weli, Shugaban gudanarwar kamfanin bunkasa man na Shell, wanda hadin gwiwa ne tsakanin kamfanin da gwamnatin Najeriya.
An ruwaito Mr Weli, a wani taron karawa juna sani kan lalata bututan mai da aka gudanar a birnin Fatakwal, na fadin cewa an kai hare-haren ne kan rijiyoyin man fetur, wanda suka lakume kaso 90 na kudaden canjin Najeriya da kudaden shigar gwamnati.
A cewarsa, tun shekarar 2012, kamfanin na Shell ya gano wasu wurare har dubu 1,160 da masu satar man ke hada-hadarsu.
Sai dai ya ce wannan mataki bai haifar da alheri ba ta yadda cikin shekarar 2017 kadai, aka yi asarar gangar mai 9,000 duk rana, sai a shekarar da ta gabata da aka yi asarar gangar mai dubu 11 yayin da a bana, aka yi asarar gangar mai 10,000.
Mista Weli ya kuma alakanta abubuwan da ke faruwa da yankin Neja Delta na rashin ci gaba, yana mai cewa akasarin mutanen da ke yankin talakawa ne duk kuwa da irin tarin arzikin da yankin yake da shi.
Jaridar Premium Times ta rawaito Mista Weli na cewa akwai yankin Neja Delta da kamfanin na Shell ya bai wa makudan kudaden da suka kai sama da naira biliyan biyu kwatankwacin miliyan 5.5 a dala, sai dai abin takaicin a cewarsa, har yanzu wannan yanki yana nan babu wani ci gaba.
Ya ce yankin yana karbar kaso 13 cikin 100 na arzikin kasa daga hannun hukumar bunkasa yankin Neja Delta, gami da wasu kudaden tallafi daga kamfanoni amma kuma wannan yanki yana nan jiya i yau.
''Yankin Neja Delta yaki samun ci gaban da ake bukata duk da irin makudan kudaden da ake warewa yankin, in ji Mista Weli.
A cewar Weli, ''Akwai bukatar mu tambayi kanmu mahimman tambayoyi domin kawo gagarumin sauyi a yankin na Neja Delta''