'Saudiyya ta bai wa Albashir miliyoyin daloli'

Asalin hoton, AFP
Tsohon shugaban kasar Sudan Omar Albashir ya amshi miliyoyin daloli daga hannun Saudiya a cewar wani jami'in tsaro a Kotu.
Tsohon shugaban ya bayyana a gaban kotu a ranar Litinin, inda ake zarginsa da aikata rashawa, zargin da lauyoyinsa suka musanta.
An hambarar da shi ne a watan Afrilun 2019 bayan ya kwashe kusan shekara 30 a kan mulki.
A watan Yunin shekarar nan ne mahukunta suka bayyana cewa an samu miliyoyin daloli cikin buhuna a gidansa.
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka cinma yarjejejiniya domin kafa gwamnatin hadaka tsakanin sojoji da farar hula.
Mene ne zargin da ake yi masa?
Ana zarginsa ne da samun "kyautuka ta haramtacciyar hanya da kuma "mallakar kudaden kasashen waje."
A watan Afrilun da ya gabata shugaban sojojin da mulkin kasar Abdel Fattah al Burhan ya bayyana cewa sun bankado kimanin dala miliyan 113 daga gidan Al Bashir.
Lauyoyin tsohon shugaban sun musanta zargin da ake yi masa.
An yi shirin gurfanar da shi ne gaban kotu a watan Yuli amma saboda dalilan tsaro ya sanya aka dage gurfanar da shi din.
Akwai kuma wani zargin?
A watan Mayu ne dai babban lauyan gwamnatin kasar ya bayyana cewa sun kai karar Al Bashir a kan iza wutar zanga-zanga da kuma sa hannu wajen kisan masu zanga-zangar kin jinin mulkinsa.
Zargin da ake yi masa ya biyo bayan wani bincike ne a kan mutuwar wani likita, wanda aka kashe lokacin zanga-zanga, abin da ya yi sanadiyyar kawo karshen mulkin Al Bashir a watan Afrillu.
Wani ganau ya bayyana wa BBC cewa duk da cewa likitan ya daga hannayensa yana yi wa 'yan sanda bayanin cewa shi likita ne amma suka harbe shi.










