Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana neman mutum 17 da suka nutse a teku a Legas
Hukumomi a jihar Legas ta Najeriya suna ci gaba da neman mutane 17 da jirgin ruwa ya kife da su a ranar Asabar da daddare.
A wata sanarwa da suka fitar sun ce suna zargin jirgin ya kife ne saboda ya kwaso mutanen da suka fi karfinsa sannan kuma igiyar ruwa ta ja jirgin har ya kife.
Jirgin ruwan wanda na fasinja ne ya tashi ne daga unguwar Ajah zuwa Ikorodu a yayin da hatsarin ya faru.
Hukumar agaji ta jihar ta ce an ceto mutum uku kuma an kai su asibiti, sannan kuma an gano gawar mutum daya daga cikin fasinjojin.
Mutane da dama a Legas na amfani da jiragen ruwa don kauce wa cunkoson ababen hawa, sai dai kuma hanyoyin sufurin ruwan ba a inganta su sosai ba.
A watan Yulin 2018, mutum biyar ne suka mutu bayan da wani jirgin ruwan fasinja da ya taso daga unguwar Ikorodu zuwa Victoria Island ya kife.