Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya yi sabbin nade-nade, me ya sa Abba gida-gida murna?
A wannan makon a Najeriya, an ga abubuwa daban-daban da suka faru amma a fagen siyasa dai za a iya cewa kalmomin da aka fi ji ba za su wuce majalisa da kotu da nadin mukami ba.
Jihohin Bauchi da Kano da shugabancin kamfani mai muhimmanci a kasar sun mamaye duk wasu zantukan siyasa, a shafukan sada zumunta da ma hirar fatar baka.
1. Kotin koli ta tabbatar da takarar Abba gida-gida
Ranar Talata 18 ga wannan watan na Yuni ne kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sahihin dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano.
A baya dai, Ibrahim Al-Amin (Little) ya kalubalanci hallaccin takarar Abba K Yusuf kuma ya maka jam'iyyar PDP a kotu inda ya ce jam'iyyar ba ta yi zaben fitar da gwani ba.
Ya yi nasara a wata kotu a Kano, amma Kotun Daukaka Kara a Kaduna ta yi watsi da bukatarsa, hukuncin da alkalan Kotun Kolin suka tabbatar.
Abba ya nuna murnarsa inda ya shaida wa BBC cewa "nasarar da ya samu daga Allah ne".
2. Buhari ya yi sabbin nade-nade
An wayi gari ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni da labarin nada sabon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da nada Mele Kolo Kyari, a matsayin shugaban kamfanin na 19 kuma magajin Maikanti Baru, wanda zai bar aiki a watan gobe.
Kafin dora shi a mukamin, Mele Kyari shi ne shugaban bangaren harkokin danyen mai na kamfanin, kuma wakilin Najeriya a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC.
Nada Mele Kyari shugaban NNPC dai shi ne nadi na biyu da Shugaba Buhari yayi tun bayan sake hawansa mulki a karo na biyu. Mukami na farko da ya bayar shi ne sake dora Akanta-janar na kasar Ahmed Idris.
3. Shugaban Majalisar dattawa ya 'fusata' 'yan APC
Shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya fuskanci matsin lamba bayan da ya nada Festus Adedayo a matsayin mai bashi shawara na musamman kan yada labarai.
Wasu masu fafutuka kuma magoya bayan gwamnatin Buhari sun yi korafi kan nadin Adedayo wanda suka ce "ya yi kaurin-suna wurin sukar gwamnati da Shugaba Buhari".
Hatta Uwargidan shugaban, Hajiya Aisha Buhari ta yi shagube a shafinta na Twitter inda ta dora wani hoton bidiyo da ke nuna daya daga cikin masu fafutukar siyasa a kasar kuma ma'abocin shafin na Twitter yana korafi kan bai wa Festus Adedayo matsayin.
Kwanki biyu bayan sanar da nadin, Sanata Lawan ya sanar da cire Festus daga mukamin.
4. An zabi kakaki biyu a majalisar dokokin Bauchi
Takaddama ta barke ranar da aka bude sabuwar majalisar dokokin jihar Bauchi, inda bangarorin da ke hamayya da juna suka zabi shugabanni daban-daban.
'Yan majalisa 11 na bangaren Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar PDP sun zabi Alhaji Abubakar Y. Suleiman, wanda dan jam'iyyar hamayya ne ta APC.
To amma fa ba shi jam'iyyar ke so a matsayin kakakin majalisar ba.
Su kuwa wasu 'yan majalisar 20 da ke goyon bayan tsohon gwamna Muhammad Abubakar, sai suka zabi Kawuwa Shehu Damina a matsayin na su kakakin.
Jam'iyyar adawa ta APC ce ke da rinjaye a majalisar don haka akwai yiwuwar cewa za a ci gaba da samun rikici game da ayyukan majlisar, da ma tsakanin majalisar da bangaren zartarwa.
5. Haka batun yake a jihar Edo
Makamancin wannan ne ya faru a jihar Edo inda 'yan majalisa tara daga cikin 24 da ke goyon bayan Gwamna Godwin Obaseki suka zabi Frank Okiye a matsayin kakakin majalisar jihar.
Sai dai 'yan majalisa 15 da ke biyayya ga shugaban APC na kasa Adams Oshimhole, wanda ke takun-saka da gwamnan, sun yi Allah-wadai da matakin suna masu cewa ba a basu dama sun shiga zauren ba.
Jam'iyyar APC ta kasa dai ta fitar da sanarwa tana yin Allah-wadai da dukkan abubuwan da suka faru a jihohin na Bauchi da Edo.