Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana jimamin cika shekara 20 da rasuwar Dokta Mamman Shata
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2
Jama'a da dama musamman a kafofin sada zumunta na ci gaba da nuna alhini bayan cika shekara 20 da rasuwar shahararren mawakin Hausa Dokta Mamman Shata Katsina.
Shata ya rasu ne a ranar 18 ga watan Junin shekarar 1999 a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Jama'a da dama a shafukan sada zumuntar na tunawa da shi da wakokinsa da gudunmuwar da ya bayar wajen ci gaban harshen Hausa da nishadantar da jama'a.
Wane ne Mamman Shata Katsina?
- An haife Shata a garin Musawa a jihar Katsina a shekarar 1923
- Ya yi tallan goro da alewa lokacin da yake saurayi
- Ya shafe fiye da shekara 50 yana salon wakar baka
- An rubuta dimbin takardun da kasidu game da rayuwarsa
- Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya ta ba shi digirin girmamawa
- Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta MON
- Ya yi wakoki a fannoni daban-daban na rayuwa
- Ya yi dimbin wakoki wadanda ya ce shi kansa bai san adadinsu ba
- Ya ziyarci kasashe da dama ciki har da Amurka da Birtaniya da Saudiyya
- Ya bar 'ya'ya 19 da kuma jikoki da dama
- An binne shi ne a Daura.
Ku ma za ku iya bayyana yadda za ku iya tuna da wannan shahararren mawakin a shafinmu na Twitter.