Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ake nufi da kaciyar mata?
An wallafa
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Majalisar Dinkin Duniya na kira da a kawo karshen kaciyar mata a yau (6 ga Fabrairu), ranar da aka ware don yaki da kaciyar ta mata.
An yi kiyasin cewa mace daya a cikin mata 20 ne aka yi wa wani nau'i na kaciya.
An fi yin kaciyar a wasu sassan Afirka da Gabas ta Tsakiya da Asiya. To amma, mece ce kaciyar mata?