An daure Farfesan da ya nemi yin lalata da dalibarsa a jami'ar OAU

Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

Asalin hoton, OAU

Bayanan hoto, Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su
An wallafa

Wata babbar kotu ta tarayya da ke jihar Osun a kudu maso yammacin Najeriya ta yanke wa wani malamin jami'a Farfesa Richard Akindele hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari.

Kotun ta yanke hukunci kan farfesan na Jami'ar Obafemi Awolowo ne bayan ta same shi da laifin yunkurin yin lalata da wata dalibarsa mai suna Ms Monica Osagie.

Wannan hukunci ya zo ne bayan babbar kotun ta kammala bin bahasin zargin da ake yi wa Farfesa Richard Akindele.

Ms Osagie ta zargi Farfesan da yunkurin yin lalata da ita tana mai cewa ya sha alwashin kayar da ita a kwas din da yake daukarsu idan ba ta yarda da shi ba.

Daga bisani ne hukumomin Jami'ar Obafemi Owolowo suka kafa kwamiti domin bincikar sahihancin wata hirar waya da dalibar ta nada wadda ta ce tsakanin ta ne da malamin jami'ar.

Jami'ar ta kori babban malamin bayan samun sa da laifin neman yin lalata da dalibar domin ba ta damar cin jarrabawa.

Mataimakin shugaban jami'ar Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya ce an kori Farfesa Richard Akindele ne bayan da ya amsa laifin kulla alaka da daya daga cikin dalibansa ta hanyar ba ta dace ba.

"Farfesa Akindele ya nemi yin lalata da Monica Osagie domin sauya maki kashi 33 da ta ci zuwa adadin da zai ba ta damar tsallakewa," a cewar mai magana da yawun jami'ar Mr Ogunbodede.

A watan Afrilu ne aka dakatar da Mr Akindele domin gudanar da bincike kan batun.

Muryar ta Farfesa Akindele, wanda ke koyarwa a sashen harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi na jami'ar, ta bazu a shafukan sada zumunta.

Lamarin dai ya janwo ce-ce-ku-ce a kasar tare da nuna damuwa kan halayyar wadansu malamai game da dalibansu.

Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami'o'in Najeriya.

Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su