Sojin sama na Nijar na mutuwa a wajen horo

Bayanan sautiRahoton Tchima Illah Issoufou
An wallafa

Latsa alamar Lasifika a sama domin sauraren rahoton Tchima Illah Issoufou

Wasu 'yan Nijar sun yi barazanar daukar mataki na shari'a kan yadda 'ya'yansu ke mutuwa a yayin samun horon kwarewar aikin sojin sama.

Wannan na zuwa bayan mutuwar wani mai neman kwarewa a aikin sojin sama na kasar a wajen horon.

Kungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwa kan yawan mace-macen da ake samu na sojojin saman kasar a sanadiyar bayar horon.

Mahukuntan Nijar sun ce sun kaddamar da bincike tare da bayar da umurnin dakatar da dukkan ayyukan sojojin da ke bayar da horon ga sojojin na sama.