Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ceto matashin da ya yi kwana 49 yana watan gaririya a teku
Wani matashi dan Indonisiya wanda ke kula da wata bukka ta musamman ta kamun kifi wadda ake sanya wa a teku ya rayu tsawon kwana 49 a teku ta hanyar dafa kifin da yake kamawa.
Aldi Novel Adilang yana cikin bukkar ne a wani wuri mai nisan kilomita 125 daga bakin gabar tekun Indonisiya a tsakiyar watan Yuli lokacin da wata iska mai karfi ta kada bukkar matashin mai shekara 18 zuwa can cikin teku ya yi ta watan-gaririya.
Haka ya yi ta nitsawa cikin tekun har nisan dubban kilomita zuwa kusa da tsibirin Guam na tekun Pacific wanda ke karkashin Amurka, har sai da wani jirgin ruwa na kasar Panama ya ceto shi.
Matashin mai shekara 18 wanda dan tsibirin Sulawesi ne na kasar Indonisiya, yana aiki ne a wata bukka ta musamman ta kamun kifi da ake sanyawa a cikin teku tana yawo, ba tare da wani inji ko abin tukin kwale-kwale ba.
Aikinsa shi ne ya kunna fitilun bukkar, wadanda aka tsara su yadda za su jawo hankalin kifaye, wato kamar tarko, kamar yadda jaridar Jakarta Post ta ruwaito.
Tarkon wanda aka tsara shi kamar bukka yana yawo ne a kan teku amma kuma ta can kasa an daddaure shi da igiya a ciyayin karkashin teku.
Kowa ne mako akwai wani daga kamfanin da matashin yake aiki da yake zuwa can cikin tekun ya kai masa abinci da ruwan sha da kananzir, sannan kuma ya tafi da kifayen da ya kama.
'Ya rika kuka'
A ranar 14 ga watan Yuli wata iska mai karfin gaske ta yi gaba da bukkar ta Mista Adilang, ya yi ta yawo a kan teku.
Kasancewar kayan abincinsa ba su da waya, sai ya rika kama kifi yana gasawa da katakon da aka yi dangar bukkar.
Ba a san yadda aka yi kishirwa ba ta yi masa illa ba.
''Ya ce hankalinsa ya tashi ya ji tsoro har ya rika kuka a lokacin da bukkar take yawo da shi a teku,'' In ji Fajar Fidaus wani jami'in diflomasiyya na Indonisiya a birnin Osak na Japan, kamar yadda ya gaya wa jaridar Jakarta Post.
Mahaifiyarsa ta gaya wa kamfanin dillancin labarai na AFP yadda ta samu labarin bacewar dan nata.
''Mai gidansa ya gaya wa mijina cewa ya bata,'' in ji Net kahiking. ''Shi ke nan muka bar wa Allah al'amarin muka rika addu'a.''
A ranar 31 ga watan Agusta, Mista Adilang ya aika da sakon oba-oba na neman agajin gaggawa lokacin da ya ga jirgin ruwan MV Arpeggio a kusa.
Daga nan ne mutanen jirgin ruwan na Panama suka ceto shi daga yankin tekun na tsibirin Guam.
Matukin jirgin ruwan ya tuntubi jami'an tsaron gabar tekun Guam wadanda su kuma suka ba shi dama ya kai shi Japan, inda jirgin zai je, kamar yadda wata sanarwa daga karamin ofishin jakadancin Indonisiya a Osaka ta bayyana.
A ranar shida ga watan Satumba Mista Adilang ya isa Japan daga nan kuma bayan kwana biyu aka mayar da shi Indonisiya inda aka hada shi da iyayensa. An ce yana cikin koshin lafiya yanzu.
''Yanzu ya komo gida kuma a ranar 30 ga watan Satumba zai cika shekara 19 - za mu shirya masa liyafa a ranar,'' in ji mahaifiyarsa.