Yaron da ya kirkiri wata fasaha ta korar Zakuna

Bayanan bidiyo, Bidiyon yaron da ke fatattakar Zakuna
An wallafa

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Richard Turere mai shekara 18, makiyayi ne dan kabilar Maasai wanda ya yi wani abun al'ajabi.

A lokacin da yake shekara 11 ya kirkiri wata na'ura mai ban al'ajabi ta hana Zakuna kai wa shanunsu da awakinsu hari, ganin yadda zakunan ke kashe musu a kalla dabbobi tara a duk mako.

Wannan wani bangare ne na shirin 'Masu Fasahar Kirkira na BBC' wanda Gidauniyar Bill da Melinda ta dauki nauyi.