Hotunan rayuwar marigayi Isyaka Rabi'u

An wallafa

Marigayin, wanda fitaccen malami ne kuma dan kasuwa, ya rasu yana da shekara 90 a wani asibiti a birnin Landan.

Hotunan rayuwar Isyaku Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, An haifi marigayi Isyaku Rabi'u a 1928 ga iyalan Muhammadu Rabi'u Dan Tinki, wanda mai wa'azin addinin musulunci ne daga Bichi cikin jihar Kano a Najeriya.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Daga 1936 zuwa 1942, marigayin ya halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur'ani da Larabci.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabi'u tare da abokinsa shararrarren dan kasuwa marigayi Nababa Badamasi
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaku Rabi'u da 'ya'yansa, wato Rabiu Isyaku Rabiu shugaban jirgin sama na IRS da Abdulsamad Rabiu shugaban BUA da kuma Nafiu Rabiu shugaban Kamfanin Isyaka Rabiu and Sons.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Marigayi Isiyaka Rabiu tare da tsohon Firaministan Pakistan Nawaf Shariff.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabi'u tare da shugaban darikar Kadiriyya na Afirka, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Wannan hoto ne na Khalifa Isyaka Rabu'u da shugaban kungiyar 'yan Izala na Najeriya, Sheikh Bala Lau, a wata ganawa da suka yi.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, A wannan hoton kuma, Khalifa Isyaka Rabi'u ne da mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka, wato Aliko Dangote
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabi'u tare amininsa marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabi'u tare da Sarkin musulmi, Abubakar Sa'ad na III, a wata ganawa da suka yi
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Khalifa Isyaka Rabi'u tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a wata ganawa da suka yi
Hotunan rayuwar Isyaka Rabi'u

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, A wannan hoton kuma, Khalifa Isyaka Rabi'u ne a wajen Wazifa