An tube dan Sule Lamido daga sarautar Hakimi

Asalin hoton, Facebook/ Santuraki Hakimin bamaina
Masarautar Dutse da ke jihar Jigawa a arewacin Najeriya ta tube Hakimin Bamaina, Mustapha, Lamido daga mukaminsa bisa zarginsa da hada harkar sarauta da siyasa.
A cewar masarautar za ta sanar da sabon Hakimin da zai maye gurbinsa a nan gaba.
Alhaji Mustapha dai da ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido.
Majalisar masarautar Dutse ce ta amince da tube wa Alhaji Mustapha Lamido rawaninsa na hakimcin Bamaina.
An tube shi ne bayan masarautar ta fara dakatar da shi daga mukaminsa na Hakimi.
Wata sanarwar da ta fito daga majalisar Masarautar Dutsen, wadda Sakatarenta Ahmadu malami ya rattaba wa hannu ta zargi Alhaji Mustapha Lamido da shiga harkar siyasa dumu-dumu, alhali yana basaraken gargajiya.
An dauki Sarakunan gargajiya a matsayin iyayen kasa, wadanda ba ruwansu da harkar siyasa.
Sanarwar ta jaddada cewa sai da masarautar Dutsen ta tabbatar da shigar Mustapha Lamido siyasa dumu-dumu, kafin ta dauki matakin sauke shi.
Masarautar ta dogara ne wajen dakatar da Alhaji Mustapha daga mulki bisa wata shara'a ta wani zargi na aikata ba daidai ba a shakara 2016.
An zarge shi da gudanar da wasu kwangiloli na mahaifinsa, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, inda ake shara`ar a wata kotun tarayya.
Sai dai dukkaninsu sun musanta zargin, amma har yanzu maganar na kotu.
Masarautar ta ce hakan ya saba wa doka da tsarin aikin gwamnati.
Zuwa yanzu dai babu wani martani da ya fito daga Alhaji Mustapha Lamido.
Sai dai wasu magoya bayan basaraken na mamakin zargin da ake ma sa na shiga harkar siyasa, suna cewa ba su ga laifinsa ba ko da ma ya shiga harkar siyasar, ganin cewa tun a bariya aka dakatar da shi.
Magoya bayan sun yi zargin cewa watakila kora-da-hali masarautar ta nemi yi ma sa.
Wasu na zargin cewa ana rabewa ne da guzuma don a harbi karsana, wato bita-da-kulli a fakaice ake yi da nufin bakanta wa mahaifinsa tsohon gwamnan Jigawan, Alhaji Sule Lamido, wanda a halin da ake ciki yana neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya, a karkashin jam`iyyar PDP.










