World Cup: Sabbin rigunan Super Eagles sun 'burge' jama'a

An wallafa

Najeriya ta nuna wa duniya sabbin kayan da 'yan wasan kwallon Najeriya za su sakawa, kuma kamfanin Nike ne aka ba kwantiragin yin sabbin kaya.

Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, A daren jiya Laraba ne Kamfanin Nike ya fitar da sabbin kayan da 'yan wasan babbar tagawar kwallon kafar Najeriya za su saka a gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Rigunan dai kusan iri uku ne: akwai mai launin kore gaba daya, sannan akwai mai launin kore da ratsin fari, hannayenta kuma launin baki da ratsin fari.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Daga gefen hagu a gaban rigar an yi tambarin Super Eagles, daga gefen dama kuma aka yi tambarin kamfanin wato Nike.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Rigar na da sabon tsari da wasu suka yaba da shi, amma wasu kuma sun ce zane ya yi yawa. Kamfanin Nike ne dai ya tsara wannan kayan gaba dayansu.
John Mikel Obi sanye da daya sabuwar rigar da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta fitar.

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Sai farin wando shi ma mai dauke da tambarin Super Eagle da alamar Nike, sai koriyar safa, a takaice dai launin kayan kusan irin na tutar Najeriya ne, kuma ya yi kama da wanda 'yan wasan suka saka a watan Nuwambar shekarar 1995 lokacin da suka yi rashin nasara da ci 1-0 a karawarsu da Ingila a Wembley.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Sabbin kayan sun ja hankalin masu goyon bayan kungiyar sosai, har ta kai wasu na zolaya da cewa lallai Najeriya ta ma riga ta lashe gasar kwallon kafa ta duniya ta 2018 da za a yi a Rasha.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, To 'yan Najeriyan dai na tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan sabon samfurin kaya da aka fitar.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Kungiyar Super Falcons ta mata ma ba a bar su a baya ba, inda su ma an fitar da sabbin rigunan da za su rika sakawa a bikin na Landan.
Super Eagles New Jersey

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, Wannan ita ce rigar 'track suit' da 'yan wasan Najeriya za su rika saka wa a wasannin kwallon kafa daga yanzu.