Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump ya yi amai ya lashe
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta koma cikin tsarin yarjejeniyar Paris, ta sauyin yanayi, idan za a baiwa Amurkar dama mai kyau.
Mr Trump ya ce a na hukunta masana'antun Amurka bisa rashin adalci a dalilin yarjejeniyar da ke aiki yanzu.
Ya ce "yarjejeniya ce da bani da damuwa a kanta, sai dai a baya na damu a kan yarjejeniyar da su ka sa ma hannu saboda kamar kullun, sun dauki mataki mai rauni ne a wancan lokacin. Amma akwai yiwuwar za mu iya komawa yarjejeniyar."
A watan Yunin bara ne Mr Trump ya sanar cewa kasarsa za ta janye daga yarjejeniyar da ke kokarin ganin an magance dumamar yanayi.