Buhari ya nada sabon shugaban hukumar NIA

Buhari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Buhari ya nada Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar leken asiri ta NIA.
An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Ahmed Rufa'i Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar leken asiri ta NIA.

Sanarwar nadin ta fito ne daga fadar shugaban, dauke da sa hannun Femi Adesina, mashawarcin shugaban kasar kan harkokin yada labarai.

Kafin nadin Ahmed Rufa'i Abubakar kan wannan sabon mukami, shi ne babban mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin kasashen waje.

Shugaba Buhari ya kori tsohon Darakta Janar na hukumar ta NIA ne Ayo Oke, a watan Oktoban bara kan zargin rashawa inda aka gano wasu kudade da aka boye a wani gida a Lagos, sama da dala miliyan 43 wadanda ya yi ikirarin mallakin hukumar ne.

Sanarwar ta ce sabon shugaban na NIA ya samu kwarewa a Majalisar Dinkin Duniya a fannonin da suka shafi wanzar da zaman lafiya da sasantawa da diflomasiya da mutunta doka da kuma kare hakkin dan adama.

Sannan kafin nadinsa Abubakar ya taba zama babban mai bada shawara ga rundunar hadin guiwa ta MNJTF mai hedikwata a Ndjamena kasar Chadi da ke fada da Boko Haram.

Abubakar ya yi karatun digirinsa na farko da na biyu kan Faransanci da adabi, duka a jami'ar Bayero, Kano. Kuma ya kware a harshen Ingilishi da Arabic.