Hotunan abin da ya faru a Nigeria a makon jiya

An wallafa

Hotunan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a sassan Najeriya daban-daban a makon jiya.

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yayin da ya gana da shugabannin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata .

Asalin hoton, Facebook/PDP

Bayanan hoto, Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar yayin da ya gana da shugabannin jam'iyyar PDP a Abuja ranar Talata
Wani dan Najeriya, wanda yake cikin mutum 400 da aka dawo da su daga kasar Libya a kokarinsu na zuwa nahiyar Turai yin ci rani, ya koma wurin iyalansa a jihar Edo ranar Alhamis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani dan Najeriya, wanda yake cikin mutum 400 da aka dawo da su daga kasar Libya a kokarinsu na zuwa nahiyar Turai yin ci rani, ya koma wurin iyalansa a jihar Edo ranar Alhamis
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da ya kai ziyara fadar Sarkin Biu bayan wani harin kunar bakin waken da aka kai kasuwar Biu a makon jiya

Asalin hoton, Borno State Government

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayin da ya kai ziyara fadar Sarkin Biu bayan wani harin kunar bakin waken da aka kai kasuwar Biu a makon jiya
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da ya halarci addu'o'in musamman da aka yi don fatan Allah Ya kawo Shugaba Muhammadu Buhari lafiya, shugaban ya kai ziyarar kwana biyu jihar ne a ranar Laraba

Asalin hoton, Facebook/ DG Media

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da ya halarci addu'o'in musamman da aka yi don fatan Allah Ya kawo Shugaba Muhammadu Buhari lafiya, shugaban ya kai ziyarar kwana biyu jihar ne a ranar Laraba
Shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jami'an gwamnatin jihar da kuma al'ummar jihar

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto, Shugaban ya samu kyakkyawar tarba daga manyan jami'an gwamnatin jihar da kuma al'ummar jihar
Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sabon Jakadan Najeriya a kasar Birtaniya, George Adesola Oguntade, yayin da ya gabatar da takardar kama aiki ga Sarauniyar Ingila Elizabeth II a fadarta ranar Laraba
Shugaban Riko na jam'iyyar PDP Ahmad Mohammed Makarfi yayin babban taron jam'iyyar wanda a yi a Abuja ranar Asabar

Asalin hoton, Twitter/PDP

Bayanan hoto, Shugaban Riko na jam'iyyar PDP Ahmad Mohammed Makarfi yayin babban taron jam'iyyar wanda a yi a Abuja ranar Asabar
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yayin da ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda jam'iyyar take gudanar da babban taronta na kasa a ranar Asabar.

Asalin hoton, Twitter/PDP

Bayanan hoto, Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yayin da ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda jam'iyyar take gudanar da babban taronta na kasa a ranar Asabar.
Matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, bayan ta halarci zaman wata babbar kotu da ke Abuja ranar Alhamis
Bayanan hoto, Matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, bayan ta halarci zaman wata babbar kotu da ke Abuja ranar Alhamis