Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ka'idojin shiga gasar waka ta BBC Hausa ta 2022
Wadanne ka'idojin shiga gasar waka ta BBC Hausa ta 2022 domin cikar sashen shekara 65 da fara watsa shirye-shirye da harshen Hausa.
1. Wannan gasar a bude take ga daidaikuwa da kuma hadakar da ba ta wuce mutum uku ba. Dole ne ya kasance duk wanda zai shiga gasar ka da su gaza shekara 18 da haihuwa. Ba a yarda ma'aikatan BBC ko iyalansu su shiga wannan gasa ba, walau a kungiyance ko daidaikuwa.
2. Ana son wadanda za su shiga gasar su rubuta waka ( mai amsa amo da kuma amfani da kayan kida) wadda za ta fito da murnar bikin cikar BBC Hausa shekara 65 da kafuwa. Dole ne wakar da za a aiko ta kasance a MP3 sannan ka da tsayinta ya wuce minti 5.
3. Domin aikewa da waka, dole ne masu shiga gasar su shigar da bayanansu ta wannan adireshi (Yadda za a shiga gasar waka ta BBC Hausa), din da ke shafinmu na bbchausa.com. A nan ne za a samu damar sanya MP3 da ke kunshe da wakar. Sau daya ake shiga wannan gasar saboda haka mutum ya yi Nazari kafin ya tura waka. Ga mutumin da zai aika wakar a madadin mutanen da suka yi hadaka, dole ne ya yi hakan tare da izninsu.
4. Za a rufe gasar da karfe 23:59 agogon GMT na daren 16 ga watan Fabrairun 2022. Saboda haka ba za a yi maraba da duk wata waka da aka aiko bayan nan.
Ya kamata duk wanda zai aiko da waka ya zama yana da kwafi domin ba za a dawo masa da ita ba. Za a tuntubi mutanen da suka yi nasara ne kawai.
5. Za a yi amfani da wadannan ma'aunan wajen yin alkalanci ga waka:
- Bayyana turken waka kuru-kuru; cikar BBC Hausa shekara 65 da watsa shirye-shirye;
- Dole waka ta mayar da hankali kan tarihi da shirye-shiryen BBC Hausa da rawar da take takawa wajen yada harshe da al'adun Hausawa a duniya;
- Dacewar kananan sakonnin waka da turken waka;
- Dacewar Rauji (karin murya ko amsa-amon murya) da kidan wakar da aka rera;
- Amfani da harshe da azanci da fasahar waka;
- Amfani da dabarun janhankali ko adon waka;
6. Bisa doron wadannan ma'aunan da aka lissafa a sama, ma'aikatan BBC za su zabi wakoki guda 30 wadanda suka yi fice daga cikin wadanda aka aiko da su. Daga nan kuma sai alkalan gasar ciki har da ma'aikacin BBC, za su zabi wadanda suka yi fice guda 3 sannan kuma za su zabi guda 12 wadanda su ma sun yi fice amma ba su iya kai wa ga nasarar shiga cikin ukun farko ba. A watan Maris ne kuma za a sanar da wadanda suka yi nasarar kasancewa a sahun ukun da suka yi nasara. BBC za ta yi amfani da sauran 12 da su ma suka cancanci yabo a tsawon watanni 12 a ci gaba da murnar cikar sashen Hausa na BBC shekara 65 da kafuwa.
7. Wakar da ta zamo ta farko za ta samu kyautar $2,000 sannan ta biyu za ta samu $1,500 inda wanda ta zo na uku kuma za ta karbi kyautar $1000. Akwai yiwuwar BBC ta sanya ko wallafa wakokin uku da suka yi fice da ma sauran shabiyun da suka yi fice amma ba su kai ga nasara ba, a rediyo da shafukanta na intanet.
Har wa yau, sashen BBC Sounds da sauran abokan huldar BBC Hausa kamar Freeedom Radio da Radio Gotel da Rima Radio da dai sauransu ka iya watsa wadannan wakoki. Akwai yiwuwar BBC za ta gayyaci mutum ukun da suka yi nasara domin halartar wurin bikin da za a ba su kyautukan a Abuja da ke Nijeriya. Idan har za BBC za ta yi hakan to ita ce za ta dauki nauyin sufuri da abinci da wurin kwanan mutanen guda uku. Sai dai BBC ba za ta dauki nauyin karin wasu abubuwan da ba wadannan ba kamar bizar shiga Najeriya da takardu.
8. Dole ne wakar da za a aika ta dace da ka'idojin BBC na aikin jarida da ke kunshe a wannan adireshi https://bbc.com.im/editorialguidelines/%3C/a%3E. Hakan kuwa ya hada da duk wata waka da ta kunshi abubuwa kamar haka:
19. Bisa ka'idojin BBC, wakokin da masu su suka kirkira, suna da 'yancin mallaka a kansu kuma BBC za ta nemi izini domin yin amfani da su. Ka Karin bayani: https://www.bbc.co.uk/usingthebbc/terms/who-owns-the-content-i-post-or-upload/ .
20. Wadannan dokokin na England ne da Wales. BBC ce ke gudanar da wannan gasar.