Lafiya Zinariya: Yadda cutar tamowa ke addabar yara ƴan ƙasa da shekara biyar
Lafiya Zinariya: Yadda cutar tamowa ke addabar yara ƴan ƙasa da shekara biyar
An wallafa
Matsalar rashin abinci mai gina jiki da ake kira tamowa na ci gaba da addabar miliyoyin yaran da ke nahiyar Afrika.
Asusun tallafawa yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya ce kimanin yara miliyan 11 a Najeriya ke fuskantar matsanancin ƙarancin abinci, a wani rahoton da ya fitar a 2024.
Hakan ya sa suka kasance kusan kashi 50 cikin ɗari da za su iya fuskantar matsancin abinci mai gina jiki.
Sai dai gwamnatocin ƙasar da haɗin gwiwar ƙawayenta sun ƙaddamar da asusun tallafi don magance matsalar. Jihohi huɗu sun zuba tallafi a asusun, yayin da wasu tara suka yi alƙawarin bayar da nasu tallafin.