Ranar Karatu ta Duniya: 'Aure bai hana ni cimma burina na yin digirin digirgir ba'

An wallafa

Dr Atika Bala Maiyafe wadda malama ce a kwalejin ilimi ta Jihar Kano ta CEO inda take koyar da Turancin Ingilishi, ta ce ba ta yarda aure zai hana 'ya mace yin karatu ba.

Malamar dai mai dauke da digiri uku da kuma lambar yabo ta MNI, ta samu dukkan karatun nata shekaru bayan hayayyafa.

Mahaifanta sun cire ta daga makarantar sakandare ta Dala da ke Kano domin yi mata aure.

To amma bayan shekaru sai maigidanta ya karfafa mata gwiwar ci gaba da karatun inda ta koma sakandare ta kuma fara daga inda aka cire ta tun da farko.