Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taliban ta ba da umarnin yin hukuncin Shari'a ga masu laifi
Shugaban ƙungiyar Taliban Haibatullah Akhundzada ya bai wa alkalan ƙasar Afghanistan umarnin zartar da wasu hukunce-hukunce da suka haɗa da yanke hannu ko ƙafa da jefe mutane idan aka kama su da wasu muggan laifuka.
Mai magana da yawunsa ya ce za a dinga hukunta waɗanda aka kama da laifuka irin su fashi da makami da satar mutane da bore a bisa tafarkin Shari'ar Musulunci irin yadda ƙungiyar ke kallonta.
A lokacin da mulki ke hannun Taliban a shekarun 1990, an sha sukar ƙungiyar kan irin wadannan hukunce-hukunce da suka haɗa da kashe mutane a bainar jama'a.
A lokacin da suka ƙwace mulki a bara, sun yi alkawarin yin mulkin kadaran-kadan ba tare da tsaurarawa ba.
Amma tun daga sannan ƙungiyar take ta rushe duk wani abu da ya shafi haƙƙin ɗan adam.
Ƴancin mata na daga cikin abubuwan da aka fi tsaurarawa a kansu.
Shugaban gwamnatin Taliban ɗin ya ce dole ne alkalai su hukunta masu laifi kamar yadda Shari'a ta ce, idan har laifin da suka yi ɗin ya ci karo da shari'ar.
Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid a ranar Lahadi ya wallafa saƙo a Tuwita cewa "an ɗauki matakin ne bayan da Mullah Akhundzada ya gana da wasu alkahalai."
"Ku bi takardun laifukan ɓarayi da masu satar mutane da masu bore dalla-dalla," Mujahid ya ambato Akhundzada na faɗa.
Taliban ba ta faɗi ainihin irin laifuka da hukuncin ba, amma wani malamin addini a Afghanistan ya shaida wa BBC cewa a ƙarƙashin dokar Shari'ar Musulunci, hukuncin kan haɗa da yanke hannu ko ƙafa da yi wa masu laifi bulala da jefe su a bainar jama'a.
Umarnin shi ne hujja ta baya-bayan nan da ke nuna yadda Taliban ke yin tsauri kan ƴancin ɗan adam.
A makon da ya wuce ne aka haramta wa mata zuwa wuraren shaƙatawa da na wasanni a Kabul, matakin da ya sake zama ware su daga harkokin shiga jama'a.
Dama a can baya an haramta wa mata a babban birnin ƙasar zuwa wuraren motsa jiki da na wanka.
Shiga wuraren wasanni da na shaƙatawa ya zama al'amari na nuna wariyar jinsi ƙarƙashin mulkin Taliban.
Ƙungiyar ta ce ba abin tsarin Shari'ar Musulunci ne.
An samu raguwar rikice-rikice a faɗin Afghanistan tun bayan da dakarun ƙasashen waje suka janye a bara bayan da suka shafe shekara 20 ana yaƙi.
Amma ƙungiyar ta fuskanci zarge0zargen cewa tana take haƙƙin ɗan adam, ciki har da ƴan adawa da mata da ƴan jarida.
Ta sha alwashin cewa ba za ta ci gaba da tsananta wa mata ba kamar a lokacin baya daga shekarar 1996 zuwa 2001, amma rabin al'ummar na fuskantar tsanani da takura kan wasu abubuwan da za su iya yi.
An haramta wa mata yin doguwar tsafiya ba tare da muharramai ba.
Har yanzu ƴan mata da dama ba sa zuwa makaranta a mafi yawan yankunan ƙasar, duk da alkawarin da Taliban ta yi na barin su.
A yayin da mata da dama ke aiki a fannoni kamar na lafiya da ilimi, har yanzu ba a bar da yawansu koma wa bakin aikinsu ba.
A watan Mayu aka bai wa mata umarnin dole su dinga rufe fuskokinsu bainar jama'a. An yi wa mata da dama duka kan neman ƴancinsu da suka yi.
An hana Afghanistan taɓa miliyoyin dalolin ƙasar da ke ƙasashen waje a yayin da ƙungiyoyin ƙasashen duniya ke jiran Taliban ta cika alkawuran da ta ɗauka kan tsaro da gwamnati da ƴancin ɗan adam.