Illolin da rashin jituwar jinin uwa kan haifar wa jaririnta

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Illolin da rashin jituwar jinin uwa kan haifar wa jaririnta
An wallafa

Likitoci masu kula da lafiyar yara na jaddada muhimmancin sanin rukunin jinin kowanne ma'auraci don ɗaukar matakin kare jariransu daga kamuwa da wasu cutuka masu alaƙa da rashin jituwar jini.

Wata ƙwararriyar likitar yara Dr. Mariya Mukhtar Yola a hira ta musamman da BBC ta ce kamata ya yi uwaye su riƙa zuwa yin alluran riga-kafin da suka kamata a lokacin goyon ciki da kuma bayan haihuwa.

Ta ce matsalolin da rashin jituwar jini ke haifar wa jariran da aka haifa sun haɗa da cutar shawara mai tsanani wadda ke iya lalata wawalwar jariri.

Dakta Mariya Mukhtar, likitar yara a babban asibitin asa da ke Abuja