Katin zaɓenka ƴancinka: Kada ka sayar da ƴancinka

Bayanan bidiyo, Katin zaɓenka ƴancinka: Kada ka sayar da ƴancinka
Katin zaɓenka ƴancinka: Kada ka sayar da ƴancinka
An wallafa

A lokacin da babban zaɓen Najeriya na 2023 ke ƙara matsowa, BBC Hausa da tallafin Gidauniyar MacArthur ta haɗa wasu jerin shirye-shiryen bidiyo domin faɗakarwa da kuma fayyace wa al'umma lamurran da suka shafi zaɓen.

Abubuwan da muka taɓo sun haɗa da karɓar katin zaɓe, da rashin zuwa kaɗa ƙuri'a, da tayar da rikici da sauran su.

Wannan bidiyon ya taɓo illar sayar da katin zaɓe.