Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tashin farashin kaya a Birtaniya ya zarce na sauran ƙasashen Yamma
Saukar farashin kayan abinci a duniya bai janyo faduwar farashin sauran kayayyaki ba a manyan kantunan Birtaniya.
An yi tsammanin hauhawar farashin za ta sauko zuwa ƙasa da kashi 10 a watan Maris, amma tashin farashin kayyakin abinci a ƙasar ya zarta yadda aka yi tsammani.
"Za ka so ganin inda farashin kayayyaki ya sauka a faɗin duniya, za ka so a ce a haka ya faru a manyan kantina sai dai abin ba haka yake," in ji ofishin ƙididdiga na ƙasa ya bayyanawa BBC.
Ƙungiyar masu sayar da ɗaiɗaikun kayayyaki sun ce sai an samu saukar farashi na wata uku zuwa tara kafin a ga irin tasirin a shaguna.
"Yayin da farashin samar da kayayyaki ya kai kololuwa a watan Oktoban 2022, muna tsammanin farashin abincin da kotomomi ke amfani da su ya fara sauka nan da watanni masu zuwa," in ji wani mamba na ƙungiyar.
Hauhawar farashin kayyakin abinci, wanda ke auna tashin farashin, ya faɗi da kashi 10.1 a shekarar zuwa watan Maris daga kashi 10.4 zuwa cikin watan Fabirairu, wanda hakan ya kai tashin farashin abinci mafi sauri cikin shekara 45.
Hukumar da ke kula da haƙƙin masu sayan kayayyaki ta ce farashin kaya ya fi tashi cikin sauri sama da farashin kayan abinci na gama gari.
Masu fafutuka sun ce tashin farashin kayan abincin ya hi shafar talakawa sosai, yayin da suke kashe mafi yawan kuɗaɗensu a siyasan kayan cefane.
Shi ma yaƙin Ukraine ya ƙara ta'azzara abin a faɗin duniya, yayin da farashin tsaba da kayan lambu da mai suka yi tashin gauron zabi. Tashin kuɗaɗen mota da yadda ake alkinta kaya shi ma ya ƙara yawan kuɗin shigo da kaya.
Farashin kayan a wajen diloli ya fara faɗuwa, amma yakan ɗaukar lokacin kan hakan ya je kantunan sai da kaya.
Cikin abubuwan da suka yi mugun tashi a watan Maris akwai man olive da ya tashi da kimanin kashi 49, madara da kashi 39, abincin gwamgwani ya tashi da 21.
Grant Fitzner shi ne babban jami'in da ke kula da harkokin tattalin arziki na ofishin ƙididdigar wanda ya fitar da farashin, ya ce farashin abinci a duniya ya sauka, amma har yanzu bai kai ga raguwar farashin ba.
Yayin da aka tambaye shi ko farashin zai iya haura kashi goma sai ya ce "babu shakka abu ne mai yuwuwa a masarautar, amma ba ma hasashen haka."
Tashin farashin kaya a Birtaniya ya zarce na kowacce ƙasa a kasashen Yamma, ciki har da Amurka da Jamus da Faransa da Italiya. A ranar laraba alƙaluma sun nuna an samu saukar farashin a shiyyar turai zuwa kashi 6.9 a watan jiya, daga kashi 8.5.
Masu hasashe sun ce tashin farashin zai ci gaba a Birtaniya, zai ci gaba da tashi zai kuma tsaya a sama, kuma Birtaniya za ta fi fuskantar tashin farashin tsakanin shiyyar Turai ta ɓangaren makamashi da ƙarancin ma'aikata.
Da yiwuwar farashin makamashi a Burtaniya ya sauka cikin gaggawa, ya ƙara da cewa amma matsalar za ta ci gaba tsakanin ma'aikata har sai 2024.
Jane daga Blackpool ta ce wata biyar zuwa shida da suka gabata babu sauƙi cikinsu, musamman idan ta je siyayyar ƙarshen mako.
Ta shaida wa BBC cewa wani lokacin ba ta iya cin abincin kari, ko na rana.
A wajen mutane irin su Jane, tashin farashin na nufin mummunan matsai ga kasafin kuɗin da su ke yi a wata.
"A watan jiya mun samu wasiƙa da ke cewa farashin kuɗin gidan da muke biya zai ƙaru. Amma da na saurari labarai sai na ji ana maganar farashin zai sauka, ko kuma za a bayar da wani abu."
Yayin da farashin abincin ya kasance a sama, frashin man fetur ya sauka, wanda hakan ya zama sauƙi ga masu ababan hawa.
Farashin fetur da aka samu a baya mafi tashi shi ne lokacin da ya kai £1.90 a watan Yuli yanzu kuma ya yi ƙasa zuwa £1.50 a watan Maris.
Faɗuwar farashin kayan abinci baya nufin faɗuwar farashin sauran kayayyaki, sai dai saukar farashin za ta tafi a hankali.
Simon Mellin shi ne mai kamfanin Modern Milkman, wanda suke aki aiki madara, ya ce kamfanonin samar da abinci sun fuskanci tashin farashin kayayyaci a yan watannin nan, haka madara da kwai duk sun tashi.
Ya yi amannar cewa farashin abincin zai daidaita, amma zai ci gaba da zama da tsada sama da yadda yake a irin wannan lokacin a bara.
"Ba na zaton farashin zai sauka kasa kamar yadda mutane suke zato," ya shaida wa BBC.
"Ni ma ina son farashin ya sauka amma ba na zaton ya sauka da yawa nan da wata12 masu zuwa."