Matashin da ke burin zama mai zanen motocin da babu irinsu

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Matashin da ke burin zama mai zanen motocin da babu irinsu
An wallafa

Al-amin Sabitu wani matashi ne mai fasahar zane-zanen ƙayatattun motocin da babu irin su a faɗin duniya.

Matashin ɗan asalin jihar Katsina- wanda ya ce ya fara wannan aiki ne tun yana ƙaramin yaro - ya ce akwai wani kamfani a ƙasar China da ya yi magana da shi domin ƙera irin motocin da yake zanawar.

Al-amin na amfani da manhajojin fasaha wajen zana motocin nasa.

Ya ce akwai wata mota da yake zanawa, kuma yana fatan indai aka ƙera ta, to za ta kasance motar da ta fi kowace mota ƙarfi a duniya.

b