Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Da kyar idan Sancho zai kara buga wasa a United - Ten Hag
Erik ten Hag ya ce bai sani ba ko Jadon Sancho zai ƙara buga wa Manchester United wasa nan gaba.
Mai shekara 23 yana atisaye shi kaɗai ne ba tare da sauran 'yan wasa ba, bayan da ya yi iƙirarin ɗora masa laifin rashin sanya shi cikin 'yan wasan da suka buga karawa da Arsenal.
Ten Hag ya sanar cewar dalilin da bai yi amfani da Sancho ba a karawar, saboda ƙwazonsa a atisaye ya ragu.
An tambayi Ten Hag ko zai sake saka ɗan ƙwallon a wasa sai ya ce ''Ban sani ba.''
Sancho ya yi jawabi a kafarsa ta sada zumunta, amma daga baya ya goge.
Kociyan ya sanar da cewar Sancho ba zai buga karawa da Brighton ba ranar Asabar, saboda ba wata rawar da zai taka.
United, wadda ta buga wasa hudu da fara kakar bana a Premier League ta ci wasanta biyu a gida, wanda ta doke Wolves da Nottingham Forest, amma ta yi rashin nasara a waje a gidan Tottenham da kuma Arsenal.
A bara Ten Hag ya ce abu mai sauƙi ne ya yanke shawarar da za ta amfani United, inda ya ajiye Cristiano Ronaldo bayan da ya ƙi shiga wasa domin ya chanji wani a karawa da Tottenham cikin watan Oktoban 2022.
Daga lokacin Ronaldo ya koma atisaye shi kaɗai, kodayake daga baya ya koma buga wa United tamaula.
Dan kwallon tawagar Portugal da Real Madrid ya bar ƙungiyar a cikin Nuwamba, bayan wata hira da ya yi, inda ya caccaki Manchester United.
Ten Hag ya sanar a ranar Juma'a cewar United sama take kan kowanne dan wasa.