Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Malam Jamilu Yusuf Zarewa
Ku San Malamanku tare da Malam Jamilu Yusuf Zarewa
An wallafa
Filin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Jamilu Yusuf Zarewa da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya.
An haifi malamin a garin Zarewa cikin 1981.
Ya soma karatun firamare a Zarewa inda ya kammala cikin 1991. Daga nan ya tafi College of Quranic Studies ta Kano inda ya yi karatun sakandire.
Kazalika malamin ya yi karatun gaba da sakandare a Aminu Kano School of Legal Studies, yayin da kuma ya tafi Jami'ar Madina inda ya yi digirinsa na farko da Masters da kuma Digirin Digirgir.