Lewandowski ya ci wa Barcelona kwallo hudu a wasa uku a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta je ta casa Real Valladolid 4-0 a wasan mako na uku a gasar La Liga karawar mako na uku da suka fafata a Nou Camp ranar Lahadi.
Robert Lewandowski ne ya fara cin kwallo a minti na 24 da fara tamaula, sannan Pedro Gonzalez Lopez ya kara na biyu, saura minti biyu su je hutu.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Lewandowwski ya kara na uku kuma na biyu da ya ci a karawar, kuma na hudu da ya zura a raga a La Liga ta bana.
Barcelona ta ci kwallo na hudu ta hannun Sergi Roberto daf da za a tashi da hakan ya bai wa kungiyar damar hada maki ukun da take bukata.
Paez Gavira, ya buga wasan a Nou Camp, ya zama matashin dan wasan da aka haifa a 2003 da ya yi wa Barcelona wasa na 50 a tarihi kenan.
Kawo yanzu kwallo na hudu da Lewandowski ya ci wa Barcelona a gassar La Liga kenan, tun bayan da ya koma kungiyar a bana.
Tsohon dan wasan Bayern Munich bai zura kwallo ba a wasan da Barcelona ta tashi 0-0 da Rayo Vallecano ranar 13 ga watan Agusta.
To sai dai ya ci biyu a wasan mako na biyu da Barcelona ta je ta doke Real Sociedad 4-1 ranar 21 ga watan Agusta a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Tun kan karawar ta ranar Lahadi ba a yi nasara ba a kan Barcelona a wasa 16 baya, idan har ta ci kwallo aka je hutu ba tare da an farke ba.
Ta kafa wannan bajintar tun ranar 29 ga watan Afirilun 2021 da Garanada ta yi nasara a kan Barca da ci 2-1.

Asalin hoton, Getty Images










