Man City ta dare teburin Premier League

An wallafa

Manchester City ta hau kan teburin Premier League, bayan da ta caskara Bournemouth 6-1 a wasan mako na 11 a Etihad ranar Asabar.

Tun kan hutu City ta ci kwallo uku ta hannun Jeremy Doku da Bernardo Silva da kuma Manuel Akanji.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne City ta kara na hudu ta hannun Phil Foden.

To sai dai Bournemouth ta zare daya ta hannun Luis Sinisterra, daga baya City ta kara biyu a raga ta hannun Bernardo Silva da kuma Nathan Ake.

City, wadda ke rike da kofin bara ta koma ta dayan teburin Premier League da maki 27, koda yake Arsenal tana wasa a gidan Newcastle United ranar Asabar.

Gunners mai maki 24, wadda har yanzu ba a doke ta ba a kakar nan na sa ran yin wani abu kafin wasan Tottenham da Chelsea ranar Litinin.