Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulmudallib Muhammad
Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulmudallib Muhammad
An wallafa
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya yi hira ne da Sheikh Abdulmudallib Muhammad.
An haifi malamin a garin Gusau na jihar Zamfara ranar 1 ga watan Agustan 1985.
Ya fara karatunsa ne a gida wajen mahaifiyarsa da mahaifinsa, sannan ya shiga Islamiyya a unguwar Tudun wada.
Sun koma garin Biu a jihar Borno inda a can ya yi karatun firamare ya kuma ci gaba da islamiyya.
Ya yi sakandare a wata makaran a garin Biu, kana daga bisani ya koma sakandare ta Arabiyya, ya kuma kammala a makarantar sakandaren kimiyya ta Gusau.
Daga baya ya koma Kano da karatu a makarantar share fagen shiga jami'a. Ya yi Jami'ar Wudil ya kammala a 2015.
Ku kalli bidiyon don jin cikakken tarihinsa.



