‘Ina gama digiri sai na faɗa sana’ar jari bola’

‘Ina gama digiri sai na faɗa sana’ar jari bola’
An wallafa

Wani babban mai sana’ar jari bola a birnin Kaduna, ya ce akwai buƙatar ƴan kasuwa a cikin gida su zuba jari a harkar jari bola ko sake sarrafa shara, saboda ɗumbin albarkar da ke cikinta.

“Sana’ar nan tana buƙatar ƴan kasuwa su zo su sa hannun jari, su ƙarfafa mana gwiwa saboda wannan sana’a an ci gaba da ita tun tuni a wa’ansu ƙasashe,” in ji shi.

Ibrahim Abubakar Maidi ya ce harkar tana da ɗumbin albarkar da za ta samar wa ɗumbin matasa ayyukan yi.

Ya ce matuƙar aka bunƙasa sana’ar sake sarrafa shara, za a zaburar da fannonin arziƙi da na raya ƙasa kamar noma da kiwo da inganta rayuwar halittun da ke muhalli waɗanda ke fuskantar koma-baya saboda ayyukan ɗan’adam da ke janyo gurɓata muhalli.