Wace ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce ta fi gawurta a Birtaniya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wannan wata muhawara ce da aka daɗe ana yi kan wace ƙungiya ce ta fi gawurta a Birtaniya?

Shin wace ƙungiya ce ta fi lashe kofuna? wacce ce ta fi tara kuɗin shiga, ko kuma wadda ta fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta? Wace ƙungiya ce ta fi filin wasa mai girma? Wacce ce ta fi ƙarewa a mataki mai daraja a gasar premier? Ko kuma la'akari da duka.

Sai dai wannan muhawara ce da babu wanda zai kawo ƙarshen ta, saboda dole za cigaba da samun ra'ayoyi mabambanta, kuma ba dole ba ne a samu gamsuwa a jawaban.

Domin tattaunawa kan wannan muhawara, BBC ta tambayi ma'aikatanta kusan 250 a Birtaniya domin amsa wasu tambayoyi.

An tafka muhawara kan abubuwa da dama, amma a ƙarshe sai muka yi nazari tare da daddale guda 10 da za mu zayyano.

Shin za ku amince? Na san da yawanku ba za ku ji daɗin matakin da ƙungiyarku ta zo ba, amma abin da muke so ku fahimta shi ne:

a) Wannan ƙiyasi ne, kuma akwai ra'ayoyi mabambanta

b) Ba muna nufin cewa komai gaskiya ba ne

Manyan ƙungiyoyi 10 a Birtaniya da BBC ta zaɓa

  • Manchester United
  • Liverpool
  • Arsenal
  • Manchester City
  • Celtic
  • Chelsea
  • Tottenham Hotspur
  • Rangers
  • Aston Villa
  • Newcastle United

Domin samar da gamsashshen bayani, mun yi nazarin wasu abubuwa domin ganin waɗanne ƙungiyoyin ne suke kan gaba.

Wace ƙungiya ce ta fi lashe manyan kofuna?

A al'ada ana kallon ƙungiyar da ta lashe kofuna cewa gawurtacciya ce.

Idan ana maganar lashe manyan kofuna, a gasar premier ta Ingila babu ƙungiyar da ta kai Celtic da Rangers.

Liverpool ce gaba a Ingila wajen lashe kofuna, sai Manchester United ke biya mata - kuma akwai alama Liverpool za ta kamo Manchester United wajen lashe gasar Premier guda 20.

Haka kuma ta fi kowace ƙungiya lashe gasannin turai, sannan Arsenal ce ta fi lashe gasar FA.

Yadda Manchester City ke jan zarenta a ƴan shekarunan, ciki har da lashe gasar premier shida a cikin shekara bakwai da lashe kofuna uku a kaka ɗaya a kakar 2022-23.

Wace ƙungiya ce ta yawan mabiya a kafofin sadarwa?

Wasu masu tunanin irin mazan jiya ba za su damu da batun mabiya a kafofin sadarwa ba.

Amma suna da rawar da za su taka wajen gane ƙungiyar da ta fi girma ba a Ingila ba kaɗai, har da duniya baki ɗaya.

Manchester United ce ta fi yawan masu mabiya a kafofin sadarwa idan aka haɗa jimilla, akwai wasu ƙungiyoyi da suka fi mabiya a ɗaiɗaikun kafofin na sadarwa.

Manchester City ce ta fi ƙarancin mabiya a kafofin sadarwa idan aka haɗa jimilla idan aka kwatanta da ƙungiyoyin da take maƙwabtaka da su, amma ta yi fintikau titTok. Amma kuma Tottenham ta shida a jimilla, amma kuma ta fi kowacce a TikTok.

Ƙungiyoyin da ake kira "manya shida" ne suka fi yawan mabiya, amma lashe gasar premier da Leicester City ta yi a kakar 2015-15 ta ƙara mata mabiya a kafofin sadarwa, inda ta zo ta bakwai.

Wace ƙungiya ta fi samun kuɗin shiga?

Shin batu ne ake yi na kuɗi? idan kuɗin kake tunani, to lallai Machester City za ta faɗo maka a zuciya.

A wasu alƙaluma da binciken Deloitte Money League ta fitar, ta ce Manchester City ce ta fi samun kuɗin shiga a kakar 2023-24 a Ingila da fam miliyan 708, kuma ta biyu a duniya, inda take biye da Real Madrid.

Ƙungiyoyin gasar premier guda tara ne suke cikin ƙungiyoyi 20, sannan da wasu ƙarin biyar a cikin guda 30, saboda Brighton ta ƙara matsowa bayan ta fafata gasar kofin Europa a karon farko.

Wacce ce ke da filin wasa mafi girma?

Idan kuma babbar ƙungiya na nufin mafi girman filin wasa, to lallai Manchester United ce a gaba.

Wembley ne fili mafi girma mai ɗaukar mutum 90,000, amma Old Trafford ya fi girma a cikin filayen wasannin ƙungiyoyi, sannan kuma ƙungiyar ta sanar da shirinta na faɗaɗa filin ya zarce Wembley - inda za ta kashe fam biliyan biyu domin fili mai cin mutum 100,000.

61,474.

Wacce ce ta fi ƙarewa a mataki mai kyau a shekara 10 da suka gabata?

A harkar tamaula, daɗewa ana yi yana da muhimmanci.

Wannan ne abin da Machester City ta ce a shekara 10 da suka gabata. Ta ce gasar premier guda shida - har da lashe guda huɗu a jere. Yanzu tana da ƙiyasin 1.7.

A tsakanin Liverpool da Mabchester United da Arsenal da Tottenham da Chelsea babu takamaiman bambanci a matsakaici matsayi.

Da West Ham da Verton da Crystal Palace sun fi ƙarewa a tsakankanin tsakiyar teburi a shekara 10 da suka gabata.

Ba a saka Celtic da Rangers ba saboda ba sa buga gasar premier, amma Celtic ta ƙare ta ɗaya sau tara a shekara goma da suka gabata, sannan ta ƙare ta biyu a 2020-21 ga Rangers, wadda ita kuma ta kasance ta biyu sau biyar.