Yaran da ke tafiya mai haɗarin gaske don zuwa makaranta

Bayanan bidiyo, Yaran da ke tafiya mai haɗarin gaske don zuwa makaranta
Yaran da ke tafiya mai haɗarin gaske don zuwa makaranta
An wallafa

Wadannan yara ne da ke tafiya mai cike da haɗarin kuma mai nisa domin halartar makaranta a ƙasar Indiya.

Sukan yi tafiyar da ta kai ta kusan nisan kilomita ɗaya da rabi ba takalmi.

Iyayensu da malamansu sun ce suna cike da fargaba a duk lokacin da suka tafi makarantar har sai sun koma gida.