Su wane ne Tinubu ya naɗa a matsayin jakadun Najeriya?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa mutum 32 ƙari a kan mutum uku da ya sanar waɗanda su ne za su wakilci Najeriya a ƙasashen duniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga, jakadun an kasa su gida biyu wato ma'aikatan diflomasiyya 15 da waɗanda ba maikatan diflomasiyya ba guda 17.

Shugaba Tinubu ya aike da sunayensu ga Majalisar Dattawan ƙasar domin tantancewa.

Mutanen da aka naɗa sun haɗa da tsohon shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya, Farfesa Mahmud Yakubu da kuma tshon mai taimaka wa shugaba Jonathan, Rene Omokri.

Jerin sunayen jakadun

Sanarwar ta Bayo Onanuga dai ta ce akwai mata guda 10 a jerin sunayen inda huɗu daga ciki jami'an hulɗar jakadanci ne sai kuma shida waɗanda ba jami'an hulɗar jakadancin ba ne.

Jerin sunayen kuma ya haɗa da sunayen tsaffin gwamnoni da ministoci da tsoffin kwamishinonin jihohi da kuma tsoffin sanatoci da dai sauran su.

Jerin sunayen waɗanda ba jami'an diflomasiyya ba ne:

  • Barrister Ogbonnaya Kalu - lauya daga jihar Abia
  • Reno Omokri - tsohon mai taimaka wa shugaba Jonathan daga jihar Delta
  • Mahmud Yakubu - Tsohon shugaban hukumar INEC daga jihar Bauchi.
  • Erelu Angela Adebayo - Tsohuwar matar gwamnan jihar Ekiti
  • Ifeanyi Ugwuanyi - Tsohon gwamnan jihar Enugu
  • Tasiu Musa Maigari - Tsohon kakakin majalisar dokon jihar Katsina
  • Yakubu N. Gambo - Tsohon kwmaishina daga jihar Plateau
  • Professor Nora Ladi Daduut - Tsohon sanata daga jihar Plateau
  • Otunba Femi Pedro - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Lagas
  • Chief Femi Fani-Kayode - Tsohon ministan sufurin jiragen ƙasa daga jihar Osun
  • Barrister Nkechi Linda Ufochukwu daga jihar Anambra
  • Fatima Florence Ajimobi - Tsohuwar matar gwamnan jihar Oyo
  • Lola Akande - Tsohon kwamishinan jihar Lagas
  • Grace Bent - Tsohuwar sanata a Adamawa
  • Victor Okezie Ikpeazu - Tsohon gwamnan jihar Abia
  • Senator Jimoh Ibrahim - Ɗan kasuwa kuma sanata mai ci daga jihar Ondo.
  • Ambassador Paul Oga Adikwu - Daga jihar Bneue.

Ma'aikatan diflomasiyya

  • Enebechi Monica Okwuchukwu (Abia)
  • Yakubu Nyaku Danladi(Taraba)
  • Miamuna Ibrahim Besto(Adamawa)
  • Musa Musa Abubakar (Kebbi)
  • Syndoph Paebi Endoni(Bayelsa)
  • Chima Geoffrey Lioma David(Ebonyi)
  • Mopelola Adeola-Ibrahim(Ogun)
  • Abimbola Samuel Reuben(Ondo)
  • Yvonne Ehinosen Odumah(Edo)
  • Hamza Mohammed Salau(Niger)
  • Ambassador Shehu Barde(Katsina)
  • Ambassador Ahmed Mohammed Monguno(Borno)
  • Ambassador Muhammad Saidu Dahiru(Kaduna)
  • Ambassador Olatunji Ahmed Sulu Gambari(Kwara)
  • Ambassador Wahab Adekola Akande(Osun)