Abin da ya kamata ku sani kan wasan Argentina da Croatia

Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasan daf da karshe tsakanin Argentina da Croatia a Gasar Cin Kofin Duniya ranar Talata a filin Lusail.
Wasa na biyar da za su kara a tsakaninsu kuma na uku a kofin duniya, bayan da kowacce ta ci fafatawa bibiyu har da wasan sada zumunta biyu da suka fuskanci juna.
Tawagar da Lionel Messi ke jan ragama tana da kofin duniya biyu, amma dan wasan Paris St Germain bai taba dauka ba a gasa ta biyar da yake buga wa mai shekara 35 ta karshe da yake halarta.
An kuma sha yi wa Messi gorin kofi biyu, sai dai ya dauki Copa America saura na duniya - domin ya bi sahun Diego Mardona wajen yi wa kasar bajinta.
Croatia wadda ta je wasan karshe a Rasha a 2018, bata taba daukar kofin ba, inda kyaftin Luka Modric mai Ballon d'Or ke sa ran daga shi a karon farko a kasar - kuma wasa na karshe da yake halarta a babbar gasar tamaula ta Fifa.
Croatia ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da Brazil da ci 4-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a minti na 120 ranar Juma'a.
Ita kuwa Argentina ta zo wannan gurbin bayan yin waje da Netherlands a bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 4-3, bayan da suka tashi 2-2 har da karin lokaci.
Idan Croatia ta yi nasara a kan Argentina za ta zama ta biyu da za ta fitar da Brazil da Argentina a tare a Gasar Kofin Duniya a zagayen ziri daya kwale.
Jamus ce ta taba fitar da Brazil da Jamus a Gasar Cin Kofin Duniya a 2014, wadda ta lashe gasar.
Wannan shi ne wasa na 25 da Messi zai buga a Gasar Kofin Duniya, kuma zai yi kan-kan-kan da Lothar Matthaus na Jamus a yawan buga wasannin babbar Gasar tamaula ta duniya a tarihi.
Tarihin karawa tsakanin Argentina da Croatia a tsakaninsu
Gasar Cin Kofin Duniya Alhamis 21 ga watan Yunin 2018
- Argentina 0 - 3 Croatia
Wasan sada zumunta Laraba 12 ga watan Nuwambar 2014
- Argentina 2 - 1 Croatia
Wasan sada zumunta Laraba 1 ga watan Maris 2006
- Croatia 3 - 2 Argentina
Gasar Cin Kofin Duniya Juma'a 26 ga watan Yunin 1998
- Argentina 1 - 0 Croatia

Asalin hoton, BBC Sport
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Labarin da ya shafi 'yan wasan tawagogin biyu
Argentina za ta buga wasan ba tare da Marcos Acuna ba, wanda aka dakatar da kuma Gonzalo Montiel mai jinya, wanda Tagliafico zai maye gurbinsa.
To sai dai Angel di Maria da kuma Rodrigo de Paul sun murmure sarai za kuma su iya buga wasan.
Croatia ba ta da wani dan wasan da ke jinya, tuni kuma Borna Sosa da Mislav Orsic suka warke daga rashin lafiya.
Wasu batutwan da ya kamata ku sani
Wannan shi ne wasa na uku da Argentina da Croatia za su fuskanci juna a Kofin Duniya a zagayen ziri daya kwale.
Argentina ta yi nasarar 1-0 a 1998 a Faransa, yayin da Croatia ta ci 3-0 a 2018 a Rasha, wasannin da Croatia ta yi ta biyu, bayan da Faransa ta lashe kofin.
Argentina na fatan zuwa wasan karshe karo na shida, Jamus ce kan gaba a yawan kai wa wasan karshe mai takwas a tarihi.
Ba a fidda Argentina a wasan daf da karshe a baya-bayan nan, har da wanda ta fitar da Netherlands a 2014.
Argentina ta ci wasa daya ne daga bakwai baya da ta fuskanci tawaga daga Turai, inda ta yi canjaras uku aka doke ta uku - a Qatar din nan Argentina ta doke Poland 2-0.
Kuma wasa biyu daga ukun da ta yi canjaras da tawagaogin Turai a bugun fenariti ta yi nasara.
Croatia wadda ta yi rashin nasara a wasan karshe a 2018 za ta zama ta hudu daga Turai da za ta kai wasan karshe karo biyu a jere bayan Italiya (1934 da 1938) da Netherlands (1974 da 1978) da kuma Jamus (1982 da 1986 da kuma 1990).
Sau hudu Croatia na cin fenariti na raba gardama a Gasar Kofin Duniya, wadda ta fitar da Jafan da Brazil a zagaye na biyu da Quarter finals a 2022.
Argentina ce kan gaba a yin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga sau biyar a zagayen raba gardama.

Asalin hoton, Getty Images











