Man United ta yi tuntuɓe a Tottenham a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta yi nasarar cin Manchester United 1-0 a wasan mako na 25 a Premier League da suka kara ranar Lahadi.
James Maddison ne ya ci wa Tootenham ƙwallo a minti na 13 da fara wasan, hakan ya sa ƙungiyar ta haɗa maki ukun da take bukata.
Wannan shi ne wasa na uku da suka buga a bana, kuma Tottenham ta yi nasara gida da waje a Premier har da cin 4-3 a League Cup.
Tottenham da United a kakar 2024/2025
Premier League Ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairu
- Tottenham 1 - 0 Man Utd
English League Cup Ranar Alhamis 19 ga watan Disamba
- Tottenham 4 - 3 Man Utd
Premier League RRanar 29 ga watan Satumba
- Man Utd 0 - 3 Tottenham
Wannan shi ne karon farko da Tottenham ta doke United gida da waje a Premier League tun bayan 1989/90.
Karo na shida da United ta kasa cin Tottenham, wadda ta yi nasara huɗu da canjaras biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Haka kuma Ange Postecoglu ya zama koci na hudu da United ta kasa yin nasara a wasa huɗu a Premier League, bayan Unai Emery da Ruud Gullit da kuma Nuno Espirito Santos.
Ƙungiyoyin suna fama da ƴan wasan da ke jinya, inda a United ta yi rashin Ahmad Diallo da Kobbie Mainoo da Manuel Ugarte da Toby Collyer da Lisandro Martinez da Luke Shaw da Mason Mount da Altay Bayindir da kuma Jonny Evans.
A Tottenham kuwa Radu Dragusin na jinya da ya haɗa da Micky van de Ven da Dominic Solanke da Richarlison da kuma Cristian Romero.
Da wannan sakamakon Tottenham ta yi sama zuwa mataki na 12 a teburin Premier da maki 30.
Ita kuwa United ta yi kasa zuwa mataki na 15 da maki 29, wadda ta ci wasa takwas da canjaras biyar da rashin nasara karo na 12 a Premier League.











