Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane zaɓi ya rage wa Issa Tchiroma Bakary?
Ministan kula da yankuna na jamhuriyar Kamaru, ya ce za a gurfanar da jagoran 'yan adawa, Issa Tchiroma Bakary a gaban kotu bisa zargin yin tawaye da kuma haifar da rikici, biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar na ranar 12 watan Okotoba.
A cikin wata sanarwar da aka fitar a birnin Yaoundé, Ministan ya ce tashin hankalin ya samo asali ne bayan da Mista Tchioroma ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben wanda wani abu da ya saɓa wa tanadin kundin zaɓe.
A ranar Litinin ne Majalisar Tsarin Mulkin ƙasar ta ayyana Paul Biya a matsayin mutumin da ya lashe zaɓen shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Oktoba.
Majalisar ta ce Paul Biya ya lashe zaɓen ne bayan ya samu kashi 53.66% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19%.
To sai dai Issa Tchiroma Bakary ya yi watsi da sakamakon zaɓen, inda ya yi iƙrarin cewa shi ne mutumin da ya samu nasara.
Magoya bayan Tchiroma Bakary musamman al'ummar yankin Garoua na ƙasar ta Kamaru na ci gaba da gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, inda rahotanni ke cewa gomman jama'a sun rasa ransu.
Abin tambaya shi ne ko wace dama ta rage wa madugun ƴan adawar na Kamaru?
Zaɓin da ya rage wa Issa Tchiroma Bakary
Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Majalisar Tsarin Mulkin Kamaru ta ɗauki kwana 15 kafin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, shi ne sauraron dukkan ƙorafe-ƙorafen zaɓen - hakan na nufin bayan sanar da sakamakon babu wani abu da mai ƙorafi zai iya yi.
Kan hakan ne BBC ta tuntuɓi masana kimiyyar siyasa guda biyu da suka haɗa da Farfesa Ibrahim Umara, masanan kimiyar siyasa a jami'ar Maiduguri da Farfesa Abubakar Kari na jami'ar Abuja da ke Najeriya.
"Idan ya ce bai yarda ba ma to ai ba za ka daki mutum ka hana shi kuka ba amma kuma ya san cewa ba shi da ƴansanda kuma ba shi da soja. Duk da cewa Bakary da magoya bayansa sun ci buri a wannan karo to amma dole ne su yi haƙuri su tara a gaba."
"Abin da ya sa ya kamata su yi hakuri shi ne Afirka ba za ta jure wani sabon rikicin a Kamaru ba wadda kusan da ma ita kaɗai ce a yankin tafkin Tchadi ke da ɗan zaman lafiya. Jamahuriyar tsakiyar Afirka ba sa zaman lafiya. Haka ma Congo da ƙasar Tchadi da ma Najeriya," in ji Farfesa Ibrahim Umara.
Shi ma Farfesa Abubakar Kari ya ce a halin da ake ciki zaɓin da ya rage wa Issa Tchiroma shi ne ya ɗauki ƙaddara.
"Mafi sauƙin abin da zai yi shi ne ya rungumi ƙaddara amma abin kamar da wuya. Ya yarda a kan cewa an kayar da shi ya jira har zuwa wani lokaci to amma abubuwa da dama sun sauya a Kamarun da ba zai bar hakan ta faru ba," in ji Farfesa Kari.
Farfesa Kari ya kuma ƙara da cewa bisa la'akari da irin karɓuwar da Issa Tchiroma Bakary ya yi a wurin ƴan ƙasar ka iya sa dole ko dai gwamnatin Paul Biya ko kuma ƙasashen duniya su zauna da Bakary a ƙulla wata yarjejeniya.
"Idan masu bore suka ci gaba da bore sannan hakanya ƙara ruruta wutar masu tayar da ƙayar baya a ƙasar, to lallai zama da Bakary domin cimma yarjejeniya zai zama dole. Sai dai kuma abubuwan da za su iya faruwa a nan su ne za su tabbatar da komai. Amma dai ƙasar na kan siraɗi," in ji Farfesa Kari.
Wace rawa Faransa za ta taka?
Bisa la'akari da yadda Faransa ke nuna cewa duk abin da ya shafi Kamaru ya shafe ta kasancewar tsohuwar uwar gijiyarta, masana na ganin da wuya Faransar ta bar jamhuriyar ta Kamaru wadda ake ganin ita ta rage mata, za ta yi duk mai yiwuwa wajen Kamarun ba ta faɗa cikin rikici ba.
"A yanzu haka alamu na nuna Faransa na duba ɓangaren da zai fi rinjaye kafin ta bayyana goyon bayanta. A baya Faransa ta goyi bayan Paul Biya kuma za ta iya ci gaba da goyon bayansa idan ta tabbata cewa magoya bayansa za su iya sarrafa madafun iko wajen daƙile duk wata adawa da bore da za a yi masa."
To amma kuma idan suka fahimci cewa ra'ayin jama'a ya fi karkata ga Issa Tchiroma Bakary wato wannan bore da ake yi zai yi tasiri, to Faransa za ta iya karkata ga jagoran hamayyar. Amma dai lokaci ne kawai zai iya tabbatar da haƙiƙanin abin zai faru," in ji Farfesa Abubakar Kari
Kiraye-kirayen bincike kan tursasa masu zanga-zanga
Kungiyoyin kare haƙƙin bil adama na ƙasa da ƙasa da tarayyar Turai sun buƙaci mahukuntan ƙasar Kamaru da su binciki rikicin da ya ɓarke a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a faɗin ƙasar, kafin da kuma bayan an ayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasar.
A cikin sanarwa daban daban da suka fitar , ofishin kare haƙƙin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya da Amnesty International da Human Rights Watch da kuma Tarayyyar Turai sun bayyana damuwarsu kan yadda jami'an tsaro ke tunkarar masu zanga-zangar da suka mamaye tituna domin yin allwadai da abin da suka bayyana a matsayin maguɗin zaɓe.