Abin da ya sa wasu 'yan ƙwallo suka yi barazanar yin yajin aiki saboda yawan wasanni
Abin da ya sa wasu 'yan ƙwallo suka yi barazanar yin yajin aiki saboda yawan wasanni
An wallafa
Wasu daga cikin 'yan ƙwallon ƙafa maza sun ce yawan yin wasannin na iya yi musu illa ga lafiyarsu da kuma ɗorewa a sana'ar tasu, lamarin da ya sa wasu suka yi barazanar yin yajin aiki.
Wani rahoto ya gano cewa raunin 'yan wasa a manyan ƙungiyoyi guda biyar na Turai ya karu da fiye da kashi ɗaya bisa uku cikin shekara huɗu da suka wucejanyo wallon ƙafa wasu daga cikin rahotonni
Rahoto daga ƙungiyar 'yan wasa ya gano cewa wasu daga cikin manyan 'yan wasa sun shafe kashi 88 cikin 100 na shekarunsu suna yin horo ko wasanni da tafiye-tafiye, domin buga wa ƙungiyoyinsu ko ƙasashensu.
Nauyin aikin 'yan wasan na ƙaruwa yayin da gasanni ke faɗaɗa a nahiyar Turai.



